Back

‘Yan bindiga sun kashe mata mai ciki da wasu 10 a Benue

A ranar Lahadi ne wasu ‘yan bindiga suka kashe mutane 11 ciki har da wata mata mai juna biyu a ƙauyen Ole’Adag’aklo da ke ƙaramar hukumar Agatu ta Jihar Benue.

Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ne da yamma inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi suka kashe mutane 11 tare da yin awon gaba da wasu.

Shugaban Agatu, Yakubu Ochepo, wanda ya tabbatar da lamarin a ranar Litinin, ya ce, “an kashe mutane 11. Daga cikin adadin, an gano gawarwaki bakwai. An gano gawarwakin wata mata mai juna biyu, dattijo da wasu matasa biyar. Su (sojoji) sun samu nasarar dawo da sauran gawarwakin huɗu.

“Sojoji sun je can jiya (Lahadi) domin ƙwato gawarwakin. An yi harbe-harbe kuma makiyayan da ke ɗauke da makamai sun gudu suka sake haɗuwa. Ina Makurdi yanzu don bayar da rahoto ga Operation Whirl Stroke (OPWS). Muna buƙatar ƙarin hannaye. Mun ji sun kuma kama wasu a raye, sun jefa wasu cikin kogi.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?