
An harbe mutum tara a unguwar Kwasam da ke ƙaramar hukumar Kauru da kuma unguwar Gwada da ke ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna.
‘Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wasu mutane talatin da biyar da suka haɗa da wani Daraktan Babban Bankin Najeriya (CBN) mai ritaya, da ɗan uwan shi da matar ɗan uwan.
An ce sun kuma raunata mutane tara a harin da aka kai a ƙananan hukumomin biyu.
An bayyana sunan Daraktan CBN mai ritaya Zakariya Markus.
Bayanin ya nuna cewa an kashe mutane shida, an sace biyar, biyu kuma an yi musu rauni a ƙaramar hukumar Kauru yayin da aka kashe mutane uku, aka raunata bakwai, sannan aka yi garkuwa da wasu talatin a ƙaramar hukumar Igabi ta jihar.
A cewar majiyoyin, lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe goma na dare lokacin da ‘yan bindiga suka kai wa al’ummar farmaki.
Majiyoyi sun ce ‘yan bindigar sun ɗauko wasu mutane biyu, waɗanda da barazanar harbe su, matanen suka kai su gidan ma’aikacin CBN mai ritaya suka yi awon gaba shi.
Majiyar ta ce, “’yan bindiga sun je gidan iyalinsa, suka yi awon gaba da ɗan uwansa da matar ɗan uwan.
“Mazauna garin sun yi yunƙurin kuɓutar da mutanen da suka ritsa da su, amma ‘yan fashin sun yi musu luguden wuta inda suka kashe shida, biyu kuma suka raunata.
“Waɗanda aka kashe sun haɗa da Danmasani Gwaska, Mrs Giwa John, Kapishi Barmu, Ganya Ubangida, Shigama Salisu da Gani Magawata.
“Waɗanda aka yi garkuwa da su sun haɗa da Mista Zakariya Markus (Daraktan CBN mai ritaya), Mista Monday Markus (Ƙanin Daraktan CBN mai ritaya), Mrs Monday Markus (matar Monday), ɗan Mista Alhamdu Makeri da kuma Baban Fati na Kauru.”