Back

‘Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji Uku, ‘Yan Banga Biyu A Jihar Nasarawa

Al’ummar Katapka da ke karamar hukumar Toto a jihar Nasarawa sun shiga firgici sakamakon wasu ‘yan bindiga da suka mamaye karamar hukumar wadanda ake zargin sun kashe sojoji uku da ‘yan banga biyu a ranar Talata.

A ranar 1 ga watan Fabrairun na wannan shekarar ne wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kashe mutane uku tare da lalata dukiyoyi na miliyoyin naira a yankin Katapka da Okudu da ke yankin na Toto a jihar Nasarawa lamarin da ya sa rundunar sojojin Najeriya ta tura jami’anta zuwa wurin domin tabbatar da doka da zaman lafiya a yankin.

Wakilinmu ya tattaro cewa, a yayin da jami’an soji ke kokarin ganin an dawo da zaman lafiya a yankin, ‘yan bindigar sun sake kai wani sabon hari da yammacin ranar Talatar wanda ya yi sanadin mutuwar sojoji uku da ‘yan banga biyu.

Da yake yiwa ma’aikatan jarida jawabi ta wayar tarho a yau Laraba a Lafia, Shugaban karamar hukumar Toto, Abdullahi Aliyu-Tashas, ​​ya bayyana rasuwar jami’an tsaron a matsayin abin bakin ciki.

Ya ce, “’yan bindigar da ake zargin sun afkawa jami’an sojin da ke sintiri domin tabbatar da doka da oda a yankin, inda suka kashe uku daga cikin su nan take.”

“Kwanan nan ne aka kai wa al’ummar Katakpa hari, kuma a sakamakon haka, an tura sojoji zuwa Katakpa don tabbatar da zaman lafiya, amma abin takaici an kashe wasu daga cijin Sojojin a wani kwanton bauna da aka yi a ranar Talata da yamma.” Inji shi 

Ya kara da cewa tuni an tura da karin jami’an tsaro zuwa yankin domin dakile tabarbarewar al’amarin.

A halin da ake ciki kuma, kungiyar raya al’adu ta Bassa, ta wata kabila a yankin, 

ta yi kira ga gwamnan jihar, Abdullahi Sule, da ya zakulo masu kai hare-haren a kan al’umma.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Emmanuel Gbaji, wadda kuma aka rabawa manema labarai a Lafiya a yau Laraba.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Mu al’ummar Bassa ta Jihar Nasarawa da kyar muka samu murmurewa daga kaduwar harin da aka kai kauyen Okudu a lokacin da muka samu labarin harin da aka kai kauyen Katapka. Lamarin dai ya zo ne da hasarar rayuka uku da barnatar da dukiyoyi.

“Muna so mu yi kira ga mai girma Gwamnan Jihar Nasarawa, Engr. A. A Sule, a matsayinsa na babban jami’in tsaro na jihar, da ya yi amfani da kyakkyawan matsayin sa wajen zakulo wadanda suka kai wadannan hare-hare domin dawo da zaman lafiya karamar hukumar Toto.

“Muna so mu mika ta’aziyyarmu ga iyalai da ‘yan uwan ​​wadanda lamarin ya shafa, kuma muna rokon Allah ya ba su ikon jure rashin nasu. Mun yi matukar bakin ciki da rashin nasu, kuma muna addu’ar Allah ya jikan su da rahama.”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?