
‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda biyu, da wasu mazauna garin biyu tare da sace mutane kusan arba’in a wani hari da suka kai garin Kasuwa-Daji da ke ƙaramar hukumar Kaura-Namoda a jihar Zamfara.
Mazauna garin sun ce ‘yan bindigar sun kai farmaki garin ne da sanyin safiyar Talata inda suka fara harbi ko ina don tsorata mazauna garin.
Wani mazaunin garin Kaura-Namoda, Abubakar Kaura ya shaida wa jaridar News Point Nigeria cewa ‘yan bindigar sun shigo garin ne da manyan makamai da suka haɗa da bindigar kakkaɓo jirgi.
Ya ce ‘yan bindigar sun kai hari gidan tsohon Shugaban Ƙungiyar Ma’aikatan Sufurin Hanya (NURTW) na jihar, Hamisu Kasuwar-Daji inda suka yi awon gaba da ɗaya daga cikin matansa da jikokinsa.
A cewarsa, gidan tsohon shugaban ƙungiyar ta NURTW yana kusa da ofishin ‘yan sanda a garin, ‘yan bindigar sun kai hari ofishin, inda suka kwance ɗamarar ‘yan sandan da ke bakin aiki, sannan suka kashe guda biyu.
Wani mazaunin Kasuwa-Daji wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro ya ce ‘yan bindigar sun kuma kashe mazauna garin biyu a yayin harin.
Ya tabbatar da cewa kimanin mutane arba’in ne aka sace a lokacin da suke kai farmaki gida-gida.
“An kuma kashe mazauna garin biyu, ba ‘yan sanda kaɗai ba. Ya zuwa yanzu, kimanin mutane arba’in ne ‘yan bindigar suka yi awon gaba da su,” inji shi.
Ko da yake Mai Magana da Yawun Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara, Yazid Abubakar, ya tabbatar wa da jaridar News Point Nigeria harin ta wayar tarho, bai bayar da adadin mutanen da aka sace ba.
“Eh, an kai hari a Kasuwar-Daji da sanyin safiyar yau,” in ji shi. “Har yanzu ba mu tabbatar da adadin mutanen da aka sace ba amma Kwamishinan ‘Yan Sanda ya tura ƙarin dakaru domin dawo da zaman lafiya a garin.”