Back

‘Yan bindiga sun nemi Naira Miliyan 15 domin sako wadanda aka yi garkuwa da Bas din su a Kogi

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta ceto wani Godwin Oniovosa, direban daya daga cikin motocin bas guda biyu da aka yi garkuwa da su a Inele Eteke da ke karamar hukumar Olalamaboro ta jihar Kogi.

Masu garkuwa da mutanen sun yi awon gaba ne da motocin bas guda biyu na “God Is Good Motors da ABC Transport” tare da lallasa fasinjojin wadanda yawan su ya kai a kalla goma sha hudu, Kuma har yanzu ba a san inda suke ba tun ranar Asabar da ta gabata da misalin karfe uku na rana.

Majiyoyi sun nuna cewa daya daga cikin motocin God is Good Motors na dauke da fasinjoji guda goma sha biyu yayin da ABC ke dauke da mutum biyu.

An bayyana cewa, motocin bas din guda biyu sun nufi Abuja ne daga Umuahia, jihar Abia.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, SP William Ovye Aya ya tabbatar da cewa an ceto daya daga cikin direbobin, Oniovosa a wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Litinin.

A cewar sa, “Tawagar dabaru da rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta kafa, tare da ‘yan banga da mafarauta ne suka ceto direban Godwin Oyovosa.” 

A halin da ake ciki kuma, masu garkuwa da mutanen motocin biyu da aka yi awon gaban da su, sun bukaci iyalan daya daga cikin wadanda aka sace da su kai kudi Naira miliyan goma sha biyar domin su sako su. 

Wani Chude Nnamdi, wanda matar shi ke cikin wadanda aka sacen a cikin daya daga cikin bas-bas din, mai fada a ji a shafukan sada zumunta ya tayar da jijiyar wuya inda yace har yanzu ana tsare da matar tasa.

A daya daga cikin sakon shi na X, Nnamdi ya ce “Masu garkuwa da mutanen sun yi waya da safiyar yau, ta yin amfani da wayar matata kuma suna neman kudin fansa naira miliyan goma Sha biyar.”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?