Back

‘Yan bindiga sun sace ɗalibai 287 da shugaban makaranta a Kaduna

Aƙalla ɗalibai 312 da shugaban makaranta, Abubakar Isah, ne aka sace da rana tsaka a ranar Alhamis a lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari a makarantar firamare da ƙaramar sakandare ta LEA da ke Kuriga a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Jami’an makarantar da shugabannin al’umma sun shaida wa Gwamna Uba Sani, tare da wasu manyan jami’an gwamnati da suka ziyarci makarantar a ranar Alhamis, cewa an sace ɗalibai 187 a ɓangaren sakandare da kuma 125 daga ɓangaren firamare.

Ɗaya daga cikin malaman, Sani Abdullahi, wanda ya tsallake rijiya da baya tare da wasu ya ce 25 daga cikin ɗaliban dake matakin firamare sun dawo. Saura ɗalibai 287 da shugaban makarantar a hannun ‘yan fashin.

Abdullahi ya shaida wa gwamnan cewa da misalin ƙarfe 7:47 na safe, ya shiga ofishin muƙaddashin shugaban makarantar ne domin ya sanya hannu kan halartar sa, kwatsam sai ‘yan bindigar suka kewaye harabar makarantar.

“Mun shiga ruɗani; ba mu san inda za mu je ba. Daga nan sai ’yan fashin suka ce mu shiga daji, sai muka yi musu biyayya saboda suna da yawa, yayin da ɗalibai kusan 700 ke biye da mu. Lokacin da muka shiga dajin, na yi sa’a na tsere tare da wasu mutane da yawa.

“Saboda haka, na koma ƙauyen na ba da rahoton abin da ya faru. Nan take ‘yan banga da Jami’an Hukumar ‘yan Banga ta Jihar Kaduna (KADVS) suka bi ’yan fashin, amma ba su yi nasara ba.

Hasali ma ‘yan bindigar sun kashe ɗaya daga cikin ‘yan bangan; mun yi jana’izarsa ba da daɗewa ba,” inji shi.

Da yake mayar da martani, Gwamna Sani ya ce duk yaran za su dawo nan ba da daɗewa ba. “Kafin na zo nan, na yi magana da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, kuma muna yin ƙoƙari. Jami’an tsaro sun fara aiki, kuma da yardar Allah za mu kuɓutar da yaran,” inji gwamnan.

“Za mu yi duk abin da ya kamata mu yi don ganin an dawo da yaran nan lafiya, ko da kuwa za mu zo Kuriga mu zauna da ku.

“Asalin gwamnati shine kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa. Mun gane cewa muna riƙe da wannan matsayi ne a matsayin amana ga jama’a, kuma da yardar Allah za mu ƙare haƙƙin ‘yan kasa,” inji shi.

A cewarsa, a lokacin da yake Majalisar Dattawa, ya gabatar da ƙudirin kafa ‘yan sandan jiha ne saboda ya fahimci cewa babu isassun jami’ai a ƙasa.

Ya ce da ‘yan sandan jiha, kowace al’umma kamar Kuriga za su samu mutane a cikin ‘yan sanda, kuma za a basu bindigogi ƙirar AK47 domin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?