Back

‘Yan bindiga sun sace ɗaliban jami’a a Taraba

An sace ɗalibai biyu na Jami’ar Tarayya ta Wukari a Jihar Taraba.

Masu garkuwa da mutane ne suka kai hari a masaukin ɗalibai da ke wajen jami’ar da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar Litinin inda suka yi awon gaba da ɗaliban.

An ce waɗanda abin ya shafa namiji ne da mace daga Sashen Nazarin Halittu da Sashen Tattalin Arziƙi na Jami’ar.

An ruwaito cewa masaukin ɗaliban yana kan titin Wukari zuwa Zaki Biam.

Jami’ar Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jami’ar, Misis Adore Awudu, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an tattara jami’an tsaro da matasa kuma suna kan bin sahun masu garkuwa da mutanen.

A yayin taron manema labarai na gabanin babban taron jami’ar a kwanan baya, Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Jude Sammani Rabo, ya koka da cewa rashin isasshen masauki ga ɗaliban jami’ar na jefa rayuwarsu cikin haɗari.

Da aka tuntuɓi Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Taraba, David lloyanomon ta wayar tarho, bai amsa kiran ba amma ya aika da saƙon tes, yana mai cewa, “Ina cikin taro, a aiko da saƙo don Allah!”

A cikin amsar sa ga saƙon tes da aka aika, CP ya ce, “Ina buƙatar tabbatar da ko ɗalibai ne, don Allah.”

Jihar Taraba dai na ɗaya daga cikin jihohin da matsalar rashin tsaro ta shafa a ƙasar.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?