Back

‘Yan bindiga sun sace ɗaliban makarantar allo a Sokoto

Wasu ‘yan bindiga sun sace wasu ɗaliban makarantar allo da ba a tantance adadinsu ba a Gidan Bakuso da ke ƙaramar hukumar Gada a jihar Sokoto.

An ji cewa an sace ɗaliban ne daga makarantarsu da misalin ƙarfe 1 na daren ranar Asabar.

Shugaban makarantar, Liman Abubakar, ya shaida cewa ya zuwa yanzu ba a ji ɗuriyar ɗalibai 15 ba amma “har yanzu muna ƙirgawa.”

A cewar Abubakar, ‘yan bindigar sun mamaye garin ne da misalin ƙarfe ɗaya, inda suka harbe mutum ɗaya sannan suka yi awon gaba da wata mata.

“Lokacin da suke barin garin, sai suka hangi ɗalibanmu sun shiga azuzuwansu da sauri, sai suka yi awon gaba da da yawa daga cikinsu.

“Ya zuwa yanzu mun ƙirga mutane 15 da suka ɓace kuma muna ci gaba da neman ƙarin,” inji shi.

Abubakar ya ƙara da cewa ba wannan ne karon farko da ‘yan bindiga suka kai hari ƙauyen ba.

Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Gada-gabas a majalisar dokokin jihar, Kabiru Dauda, yayin da yake tabbatar da faruwar harin, ya ce ya samu kira daga ƙauyen da misalin ƙarfe biyu na dare cewa ‘yan bindiga ne suka mamaye ƙauyen.

“Na tuntuɓi hukumomin ƙananan hukumomi da hukumomin tsaro kuma na tabbata suna yin wani abu a kai,” inji shi.

An kuma ji cewa ‘yan bindiga sun kai hari tare da kashe mutane uku a ƙauyen Turba da ke ƙaramar hukumar Isa ta jihar, ciki har da hakimin ƙauyen.

Wani ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Isa, Habibu Modachi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya yi imanin cewa ramuwar gayya ce bayan da jami’an tsaro suka kai farmaki maɓoyar ‘yan bindigar kwanaki biyu da suka wuce.

Mai Magana da Yawun Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Ahmad Rufa’i, ya ce bai san da faruwar lamarin ba, amma zai tuntuɓi Jami’in ‘Yan Sandan Shiyya na ƙananan hukumomin.

An ruwaito cewa, harin ya zo ne a daidai lokacin da jihar ke shaida bikin yaye Jami’an Tsaron Al’umma, wani matakin da gwamnatin jihar ta ɗauka na daƙile ‘yan fashi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?