Back

‘Yan bindiga sun sace manajan bankin Taj

Wasu gungun ‘yan bindiga da safiyar Talata sun kai farmaki Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, inda suka sace manajan bankin Taj reshen Gusau, Malam Mansur A. Kaura a gidansa.

Blueprint ta ruwaito cewa an sace shi ne da misalin ƙarfe 12 na safe.

An ce ‘yan ta’addan sun mamaye yankin ne ɗauke da wasu muggan makamai inda suka fara harbe-harbe a iska don tsorata mazauna yankin, sannan suka je kai tsaye gidan manajan suka ɗauke shi.

Wakilin Blueprint ya ruwaito cewa ‘yan bindigar sun addabi wasu yankuna kamar su Mareri, Damba, Tsauni da kuma Samaru a cikin babban birnin jihar.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?