A ranar Talata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wani masallaci a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da wasu masallata.
An samu labarin cewa an kai harin ne a lokacin da musulmai ke gudanar da sallar jam’i mai suna Tahajjud.
Tahajjud salla ce ta musamman da musulmi ke gudanar da ita a kowane kwanaki 10 na ƙarshen watan Ramadan.
Zamfara dai na fama da munanan hare-hare tun bayan da ‘yan bindiga suka fara ta’addancin su a jihar Arewa maso Yamman.
Daidai mako guda da ya gabata, Gwamna Dauda Lawal ya tattauna da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kan yadda ake ta samun ƙaruwar fashi da aikata laifuka a jihar.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, Lawal ya bayyanawa Shugaban Ƙasa Tinubu halin da ake ciki na tsaro a Zamfara, musamman yadda ake ci gaba da kai hare-hare a wasu ƙananan hukumomi.
Rahotanni sun bayyana cewa Tinubu da gwamnan sun tattauna dabaru da matakai daban-daban domin tunkarar wannan matsala da ya haɗa da inganta tsaro, tattara bayanan sirri da kuma shirye-shiryen shiga tsakanin al’umma.
Ganawar ta kuma bayyana buƙatar magance matsalolin da suka addabe su, kamar talauci da rashin aikin yi, waɗanda suka taimaka wajen yawaitar miyagun ayyuka a jihar.
“A yau ne gwamna Dauda Lawal ya gana da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa inda suka tattauna muhimman batutuwan da suka shafi matsalar tsaro a jihar Zamfara.”
“A yayin ganawar sirrin, Gwamna Lawal ya sanar da Shugaban Ƙasar cewa, a cikin shekaru 13 da suka gabata, jihar Zamfara ta zama cibiyar ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya.
“Gwamnan ya roƙi Shugaban Ƙasa Tinubu da ya kawo wa sojoji isassun jami’ai, makamai, da kuma kayan aiki, domin sun yi ƙaranci a Zamfara. Ya kuma buƙaci isassun tallafin sojojin sama don taimakawa sojojin ƙasa.
“Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya baiwa gwamnan tabbacin bada duk wani muhimmin tallafi da kayan yaƙi ga jami’an tsaro domin tabbatar da maido da zaman lafiya a Zamfara.
“Bugu da ƙari, Shugaban Ƙasar ya sake jaddada matsayin gwamnatinsa na rashin yin sulhu da ‘yan bindiga da kuma biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane, matakin da ya yi imanin zai taimaka musu ne kawai,” inji sanarwar.