Back

‘Yan bindiga sun sace mutane 200, sun kashe jami’an tsaro 4 da mazauna ƙauye 3 a Neja

Wasu ‘yan bindiga sun sake kai hari a daren Juma’a a ƙauyen Kuchi da ke ƙaramar hukumar Munya a Jihar Neja inda suka kashe jami’an tsaro 4 da mazauna ƙauyen 3.

An ruwaito cewa jami’an 4 da suka mutu na Jami’an Tsaron Haɗin Gwiwa ne da aka girke a yankin.

Wani mazaunin ƙauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ‘yan bindigar sun yi awon gaba da mutanen ƙauyen su 200 a harin da aka kai a daren Juma’a.

Ya ce ‘yan bindigar sun haura sama da 300 a lokacin da suka mamaye al’ummar da misalin ƙarfe 7 na dare kuma suka yi ta kai hari sama da sa’o’i uku ba tare da samun tirjiya ba.

“Suna bi gida-gida suna zaɓar waɗanda suke so su tafi da su, ciki har da mata.

Sun wawashe duk shagunan da ke unguwar suka tafi da dukkan kayayyaki da abubuwan sha,” inji shi.

A cewarsa, “Sun yi galaba a kan jami’an tsaro, babu yadda za a yi su iya tinkarar ‘yan bindigar, domin ‘yan bindigar sun shigo da babura kusan 100 kuma kowanne yana ɗauke da aƙalla mutum uku. Dukkansu suna ɗauke da manyan makamai”.

Ya bayyana cewa ba wani taimako ga jami’an tsaro dake ƙauyen sai zuwa safiyar yau (Asabar) da wasu jami’an tsaro suka zo lokacin da aka riga aka yi ɓarnar.

Da aka tuntuɓi Ciyaman na ƙaramar hukumar Munya, Malam Aminu Najume, ya tabbatar da faruwar harin na Juma’a inda ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kashe jami’an tsaro huɗu ciki har da ‘yan banga na yankin.

Shugaban ya bayyana cewa ‘yan bindigar kimanin 300 sun mamaye al’ummar ne da misalin karfe 7 na dare.

Ya ƙara da cewa “suna tafiya gida gida suna ƙwacewa mutane kayansu.

“Sun kuma yi awon gaba da mutanen ƙauyen kimanin 150 da suka haɗa da mata, suka tafi da su cikin ruwan sama. A tsawon farmakin da ‘yan bindigar suka kai, babu wani taimako da ya fito daga ko’ina.”

Ya ɗora laifin ci gaba da kai hare-haren da ‘yan bindigar ke kaiwa al’umomin ƙaramar hukumarsa a kan abin da ya kira gazawar Gwamnatin Jihar Kaduna wajen ɗaukar ƙwararan matakai a kansu, yana mai jaddada cewa “idan Jihar Kaduna na yin abin da Jihar Neja ke yi, da an magance lamarin.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?