Back

‘Yan bindiga sun sace mutane 61 a wani sabon hari a Kaduna

Aƙalla mutane 61 ne rahotanni suka ce wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne da suka kai hari ƙauyen Buda da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna, suka yi garkuwa da su.

Har yanzu hukumomin jihar da na ‘yan sanda ba su tabbatar da faruwar harin ba, amma wani mazaunin yankin ya shaida a ranar Talata cewa ‘yan bindigar sun mamaye ƙauyen ne a daren ranar Litinin da misalin ƙarfe 11:45 na dare, inda suka sace mutane 61.

A cewar wani mazaunin garin, Dauda Kajuru, masu garkuwa da mutanen da yawa sun mamaye al’ummar inda suka fara harbi ba kakkautawa.

“Abin da ya faru jiya yana da ban tsoro. ‘Yan bindigar sun zo ne da nufin yin garkuwa da mutane da dama wanda zai zarce na ɗaliban makaranta a ƙauyen Kuriga da ke ƙaramar hukumar Chikun, amma saurin mayar da martanin da sojojin da ke kilomita 2 nesa da Kajuru suka yi ya taƙaita adadin.

“Yan uwana na cikin waɗanda aka sace jiya kuma bisa ga bayanin da aka samu har zuwa safiyar yau, ‘yan bindigar da waɗanda abin ya shafa ba su kai ga masaukin su ba,” inji Manyu.

Ya koka da yadda tun bayan sauke wani Kwamandan Sojoji da aka fi sani da Tega, aikin fashi ya dawo da ƙarfi a kewayen ƙauyukan ƙaramar hukumar Kajuru.

“Zan gaya muku da ƙwarin gwiwa cewa lokacin da Kwamanda Tega yake wurin, ayyukansu sun tsaya, kuma mutum na iya tafiya lokaci-lokaci ba tare da fargabar sace shi ba saboda ya san hanyoyin su da kuma yanayin ayyukansu.

“Abin taƙaici ne an cire Kwamanda Tega daga ƙaramar hukumar Kajuru lokacin da muke samun dawowar zaman lafiya a ƙauyukanmu,” inji shi.

Wani mazaunin garin, Lawal Abdullahi, wanda ya tsere daga lamarin amma matarsa ​​na cikin waɗanda abin ya shafa, ya kuma tabbatar da sace mutane 61.

Ya ce akwai maza da mata da yara da suka haɗa da wata mata mai shayarwa ‘yar sati biyu.

“Al’amarin ya girgiza ni domin ba mu ji ɗuriyarsu ba tun bayan faruwar lamarin a ranar Litinin.

“Muna kira ga gwamnati da ta ɗauki mataki kuma ta tabbatar da cewa masoyanmu sun dawo cikin gaggawa,” inji shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?