Back

‘Yan bindiga sun sake kashe mutane 49 a Zamfara

Aƙalla mutane 49 ne ‘yan bindiga suka kashe a wasu hare-hare na tsawon kwanaki biyar a Jihar Zamfara.

Marigayan, a cewar mazauna garin, an kashe su ne a ƙauyuka biyar da rikicin ya shafa a ƙaramar hukumar Anka ta Jihar Zamfara daga ranar Talata zuwa Asabar.

A cewar mazauna yankin, an kashe mutane 18 a ƙauyen Farar-Kasa; 22 a Dangulbi, biyu a Duhuwa, huɗu a Tsatsomawa da wasu uku a ƙauyukan Yar Sabaya.

Wani mazaunin garin Anka, Malam Idris Anka (ba sunansa na gaskiya ba) ya ce tun farkon makon nan ne ‘yan bindigar ke kai hare-hare a cikin al’ummomin ƙaramar hukumar.

Ya ce, “’Yan bindiga sun zama ruwan dare a wannan yanki na Jihar Zamfara. Gaskiyar magana a gare ku, mun gaji da wannan barazanar. ’Yan bindiga suna ta aiki kamar ba mu da gwamnati a ƙasar nan. Waɗannan mutane kusan komai ne a cikin al’ummominmu; su ne ‘yan sanda, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma.

“Za su iya kai hari ga kowace al’umma yadda suke so, sanya haraji a kan kowace al’ummar da suke so kuma su sace kowa a kowace al’umma kuma ba wanda ke da ikon ya ce a’a wa umarnin da suka bayar.”

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce da ƙyar ya tsere wa ‘yan bindigar da ke kan hanyar Anka zuwa Bagega a yau (Asabar) inda ya ce “’yan bindiga biyu sanye da kakin sojoji sun kafa wani shingen bincike a kan titin a yau (jiya) suna fashin masu amfani da hanyar.

Mallam Bello Muhammad, wani direban ‘yan kasuwa ne, ya roƙi Gwamnatin Tarayya da na jihohi da su kawo musu ɗauki ta hanyar samar da isassun jami’an tsaro a yankin, domin a cewarsa rashin kasancewar tsaro na taimaka wa ‘yan bindiga a ƙananan hukumomin.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?