Back

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da jama’a daga masallaci a garin Tsafe, Jihar Zamfara 

Wani ɗan unguwar mai suna Garba ya shaida cewa ‘yan bindigar sun mamaye masallacin ne da misalin ƙarfe biyar na safiyar ranar Alhamis a lokacin da mutanen ke shirin fara sallar asuba.

Garba ya ce, “Yau alhamis za mu fara sallar asuba, kwatsam sai ga su (’yan bindiga) suka shiga masallaci suka umarci kowa ya fita ya bi su.

“Kowa ya yi ƙoƙarin tserewa domin tsira da ransa amma ‘yan bindigar sun tare ko’ina kuma suka gargaɗe mu cewa za su kashe duk wanda ya yi yunƙurin guduwa.

“Na yi tsalle daga taga kuma da sauri na shiga ɗaya daga cikin gine-ginen da ba a kammala ba kusa da masallacin inda na ɓoye kaina.”

Garba ya ci gaba da cewa ‘yan bindigar sun bar baburansu nesa da masallacin don kada masallata su lura da motsinsu.

“Sun zo ne da ƙafa, inda suka bar baburansu a wajen gari don kada su jawo hankalin jama’ar yankin.” 

Ya ƙara da cewa, “Daga baya suka yi tattaki da masallatan zuwa baburansu, sannan suka tafi dasu cikin daji.

A cewar Garba, adadin masallatan da aka sace zai iya wuce talatin.

Ya ƙara da cewa “masallacin ya cika lokacin da ‘yan fashin suka kai hari a wurin kuma kaɗan ne daga cikin mu suka tsira.”

Ɗaya daga cikin shugabannin al’ummar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce jami’an tsaro na ci gaba da bin sawun ɓarayin domin kuɓutar da masu ibadar da aka sace.

Ƙaramar hukumar Tsafe dai na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin jihar da ke fama da matsalar ‘yan fashi.

Titin Tsafe-Gusau mai tsawon kilomita hamsin da shida ya zama wuri mafi haɗari a jihar inda a kullum ake sace mutane.

‘Yan bindiga da dama ne suka rasa rayukansu a ‘yan kwanakin da suka gabata a cikin ƙaramar hukumar lokacin da wasu gungun ‘yan bindiga guda biyu suka yi arangama.

Duk ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar, ya ci tura, domin an kasa samunsa ta wayar tarho, bayan an yi ta ƙoƙarin hakan.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?