Back

‘yan boko haram sun kai hari ofishin ‘yan sandan Borno, sun kashe ‘yan sanda hudu

An yi zargin an kashe ‘yan sanda hudu, da kuma sace tarin alburusai lokacin da wasu da ake kyautata zaton mayakan kungiyar IS ne na yankin yammacin Afirka suka kai hari a ofishin ‘yan sandan da ke karamar hukumar Nganzai a jihar Borno.

Mayakan ISWAP, kamar yadda jaridar PUNCH ta ruwaito tace, maharan da suka taru sun kai farmaki ofishin ‘yan sanda a garin Gajiram inda suka bude wuta kan ‘yan sandan da ke bakin aiki.

Wata majiyar tsaro da ta zanta da wakilinmu da ya nemi a sakaya sunanta domin ba shi da damar yin magana akan abin da ya faru, ta ce ‘yan ta’addan sun kuma kona wasu sassan ofishin ‘yan sanda a yayin harin da aka kai da yammacin Juma’a.

“Wasu daga cikin ‘yan sandan kuma sun yi sa’a da suka tsira daga harin ta’addancin, amma jami’an ‘yan sanda hudu da suka yi rashin sa’a sun biya farashi mai tsoka a lokacin da suke bakin aiki,” 

Majiyar PUNCH ta kara da cewa, “An samu rudani a garin mu a daren jiya lokacin da mayakan na ISWAP suka kai hari ofishin ‘yan sanda da ke Gajiram. Sun fi karfin ’yan sandan da ke bakin aiki.”

“Mun gano gawarwaki hudu na ‘yan sandan da suka rasa rayukan su da sanyin safiyar yau. Har yanzu wasu ‘yan sanda ba su dawo bakin aiki ba.”

Jihar Borno dai ta sha fama da munanan hare-hare daga ‘yan ta’adda duk da kokarin da sojoji da sauran jami’an tsaro na hadin gwiwa suke yi na dakile munanan ayyukan kungiyoyin ta’addanci a jihar.

Wata majiyar ’yan banga na yankin da ta tabbatar wa wakilin jaridar PUNCH din ta bayyana cewa maharan sun bar wurin ne kafin dakarun sojoji su iso.

“Eh, lokacin da muka samu rahoton kuma muka tuntubi sojojin da suka mayar da martani cikin gaggawa, domin dakarun su, sun yi tattaki zuwa wurin, amma abin takaici, maharan sun tsere,” in ji shi.

Da yake tabbatar da harin tare da kashe abokan aikin sa guda hudu, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Nahum Kenneth ya shaidawa PUNCH Online cewa, “Mun samu rahoton cewa ‘yan tada kayar baya sun kai hari ofishin mu na Gajiram da misalin karfe 1 na daren Jumma’at, wayewar yau Asabar 3 ga watan Fabrairu.

“Hakika ‘yan sanda hudu sun biya farashi mai tsoka a wata musayar wuta da ‘yan ta’addan a lokacin da jami’an tsaro suka yi gaggawar daukar matakin dakile harin.

“Tuni an fara samun nutsuwa a garin” in ji shi.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?