Back

‘Yan Boko Haram sun yi wa sojoji kwanton ɓauna, sun kashe shida a Borno

Aƙalla sojoji shida ne suka rasa rayukansu a wani harin ƙwantan ɓauna da aka kai musu a hanyar Biu-Buni Yadi, Jihar Borno.

Sojojin sun mutu ne dai mako guda bayan da aka yi jana’izar sojojin da aka kashe yayin da suke aikin samar da zaman lafiya a jihar Delta a maƙabartar sojoji ta ƙasa da ke Abuja.

An ruwaito cewa mayaƙan Boko Haram sun yi wa sojojin kwanton ɓauna a Kamuya, wani ƙauye kusa da Buratai, mahaifar Tsohon Babban Hafsan Soji, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya).

Wata majiyar tsaro ta ce sojojin sun rasa rayukan su kan hanyarsu ta zuwa Damaturu domin sayen mai.

“Abin baƙin ciki ne matuƙa; sun kasance sojojin 135 Special Force BN FOB a Buratai. An yi musu kwanton ɓauna a hanyarsu ta zuwa Damaturu, Jihar Yobe, domin sayen mai.”

“Abin takaici, mun rasa wani jami’i, direba, ɗan bindiga da wasu ’yan rakiya huɗu, yayin da waɗanda suka raunata ke asibiti suna karɓar magani,” inji shi.

Wata majiya mai tushe da ta tsallake rijiya da baya, ta ce yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa garin Yadi maƙwabciyarta, mahaifar Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe, ya garzaya wurin da lamarin ya faru.

“Ba zan iya kwatanta irin faɗan bindigar da aka yi ba, ‘yan ta’addan da ke da yawa sun mamaye sojojin. Da yardar Allah na tsira,” inji shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?