Back

’Yan fasa-kwauri sun kai hari kan Kwastam, sun yi awon gaba da AK47 a Kebbi

Wasu da ake zargin masu safarar shinkafa ta ɓarauniyar hanya ne sun kai hari kan jami’an hukumar kwastam a tashar Yauri a jihar Kebbi.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kwastam na Jihar Kebbi, Mohammed Tajudeen Salisu, a cikin wata sanarwa da ya fitar wa Kwanturolan Hukumar Kwastam, Iheanacho Ernest Ojike, ya ce jami’in da ke kula da tashar (OiC) ya samu rauni a harin kuma an yi awon gaba da wata bindigar AK47 guda ɗaya amma daga baya aka dawo da ita.

Ya ce maharan sun tafi da buhunan shinkafa 29 cikin 41 da Hukumar Kwastam ta kama.

Ya ƙara da cewa, an sanar da duka tawagar tashar Yauri da kuma tawagar sa ido kan wani aikin fasa ƙwauri da ake zargin ana yi a gaɓar tekun Yauri.

“Da isa wurin, an kama buhunan shinkafa ‘yan ƙasashen waje guda 41, aka tsare su, sannan aka kai su tashar.

“Bayan haka, ‘yan fasa-kwaurin sun ƙaddamar da wani harin gungun ‘yan tada zaune tsaye a tashar,” inji shi.

Ya ce da suka ga ’yan iskan, masu kula da tashar sun tuntuɓi hukumar da sauran hukumomin ‘yan uwa domin ƙarin dakaru, waɗanda suka taimaka wajen shawo kan lamarin.

PRO ya ce ’yan iskan sun lalata motar OiC, na’urorin sanyaya iska, kujeru, tebura, tagogi, ƙofofi, da sauran kayayyakin da aka samar don tallafawa ayyukan tashar.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?