
‘Yan kasuwa a babbar kasuwar sayar da kayan lambu ta Kano, Kasuwar ‘Yankaba, sun yi kira ga gwamnatin jihar da kananan hukumomin jihar da su inganta kayayyakin more rayuwa a kasuwar da kuma sauran kasuwannin jihar.
Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa, Aminu Lawal, a wata tattaunawa da yayi da ‘yan Jaridu, ya ce, kasuwar ta kara habaka da karuwar ‘yan kasuwa da kwastomomi da harkokin ciniki da kashi tamanin cikin dari tun daga lokacin da aka kafa ta a shekarar ta 1983, inda ya ce wasu ‘yan kasuwa sun koma amfani da rumfunan gaban shaguna su da gefen hanya domin nuna kayayyakin su.
Sun ce, kasuwannin, musamman ta ‘Yankaba na matukar bukatar fadadawa da kuma samar da ababen more rayuwa domin bunkasa kasuwancin su.
Sun yi kira ga Gwamna, Abba Kabir Yusuf da ya mayar da inganta ayyukan more rayuwa ya zama daya daga cikin abubuwan da gwamnatin shi ta sa gaba.
Lawal ya bayyana rashin sarari, wutar lantarki, hanyoyin sadarwa mai kyau, haraji da yayi yawa, matsalar zubar da shara da inuwa a matsayin wasu manyan kalubalen da ‘yan kasuwa ke fuskanta a kasuwar wadanda galibi ke sayar da kayan marmari da kayan asarrafa abinci kamar su barkono, tumatir, barkono mai zafi, albasa. okra, alayyaho, kabewa, latas, kabeji, kankana da sauransu.
Ya ce, ana ci gaba da kasuwanci dare da rana a kasuwar, inda ya ce galibin kayayyakin ana sauke su ne da daddare, daga karfe bakwai na yamma har zuwa kashegari da rana, kuma da karfe biyar na safe mutane sukan fara lodi da kuma yin tururuwa domin saye da sayarwa.
“Kasuwar tana aiki ko da daddare, kuma tana bukatar wutar lantarki akai-akai ko hasken rana wanda zai iya haskaka kasuwar da kuma inganta tsaro.”
“Dubban ‘yan kasuwa ne ke shiga wannan kasuwa ta cikin gida. Muna horar da matasa masu sha’awar ciniki. Amma ƙananan ƴan kasuwa sun fi yawa kuma suna buƙatar ƙarin jari domin kasuwanci.”
“An kafa kasuwar ne a shekarar 1983, kuma tsarin wancan lokacin ya kasance tsohon abu Kuma mai karewa. Yanzu kasuwar ba ta ishe mu ba, a matse ta ke, kuma ta fadada da kashi tamanin cikin dari ta fuskar kasuwanci da mutane. Tun daga wannan lokacin ba a taba fadadawa ba.
“Muna kuma buƙatar hanyoyin da suka dace na zubar da shara da sararin da za mu fito da kaya a gani, idan aka hi la’akari da ksyan abincin da muke sayarwa a kasuwar, muna buƙatar tsafyacewa domin kiyaye lafiyar al’umma.” in ji shugaban