
‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Filato guda goma sha shida da aka kora a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, sun garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara, inda suke neman ta yi watsi da hukuncin da karamar kotun ta yanke da farko na soke zaɓen su.
Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke zaɓen da aka yi wa ɗaukacin ‘Yan Majalisar Dokokin jam’iyyar PDP a Majalisar Dokokin Jihar ne saboda, kamar yadda ta ce, jam’iyyar su, a lokacin da aka yi zaben ba ta da tsarin da za ta ɗauki nauyin ‘yan takara a dukkanin zabukan.
Sai dai ‘yan majalisar da aka kora sun dage cewa har yanzu su ne mambobin Majalisar bayan nasarar da gwamnan jihar, Caleb Mutfwang, ya samu a kotun Ƙoli inda tayi hukuncin tabbatar da zaɓen shi bayan da shima karamar kotun, da kuma kotun daukaka Kara ta soke zaben shi.
‘Yan majalisar sun yi imanin cewa hukuncin Kotun Ƙoli ya wanke su.
‘Yan majalisar da aka kora sun haɗa da Bala Fwanje Ndat da Datugun Paul Naankot da dai sauran su, a cikin buƙatar da suka gabatar mai lamba CA/J/33M/2024 da CA/J/31/M/2024 a gaban kotun, sun ce bisa ga doka ta 6 ƙa’ida ta 1 na Kotun Ɗaukaka Ƙara, 2021, ya kamata a mayar da su cikin Majalisar.
Wannan na daga cikin sassaucin da lauyan su Garba Paul, SAN ya gabatar, inda ya bayyana cewa kotun sauraron ƙararrakin zaɓe da Kotun Ɗaukaka Ƙara ba su da hurumin gudanar da wannan hukuncin.
‘Yan majalisar da aka kora sun ce hujjar tasu kamar yadda take ƙunshe a cikin buƙatun su ya ta’allaƙa ne kan cewa, “Hukuncin da kotun ta yanke a ranar ishirin da hudu ga watan sha daya na shekarar da ta gabata, ba Mai tasiri bane.”
‘Yan Majalisar suna neman “kotun tayi watsi da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara mai lamba CA/J/EP/PL/SHA/62/2023, Dagogot Karyt Owen & Anor da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), & Ors a ranar 24 ga Nuwamba, 2023 , ta E.O Williams-Dawodu, Abdul-Azeez Waziri da E.O Abang, JCA.”
A cewar su, hukuncin Kotun Ƙolin da ya tabbatar da zaben da kuma ɗaukar nauyin Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya isa Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yi watsi da hukuncin da ta yanke a baya.
‘Yan majalisar, a baya sun yi yunƙurin komawa Majalisar Dokokin, matakin da ya kusa janyo rikicin siyasa a jihar ya Filato.
A halin yanzu dai, Shugaban Majalisar Jihar, Gabriel Dewan Kudagbena bai rantsar da mambobin jam’iyyar APC da suka ci gajiyar hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙarar ba.
Shugaban majalisar ya rataya hukuncin da ya yanke kan umarnin kotu da suka saɓa wa juna.