Sama da ‘yan Nijeriya miliyan ɗaya da dubu ɗari shida ne suka nemi rance a Shirin Ba Da Lamuni na Mabuƙata, inji Gwamnatin Tarayya a ranar Talata.
Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Hukumar Bayar da Lamuni na Mabuƙata na Nijeriya (CREDICORP) ya bayyana hakan, inda ya ce adadin ‘yan Nijeriya miliyan 1.6 ne.
A ranar 21 ga Afrilu, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ƙaddamar da kashi na farko na Shirin Ba Da Lamuni na Mabuƙata.
Shirin zai baiwa ‘yan ƙasa masu aiki damar samun lamuni don sayayya masu mahimmanci.
Makonni uku bayan fara shirin, shugaban na CREDICORP ya ce adadin masu nema da aka samu zuwa yanzu da yawa.
“Abun mamaki ne. Ba mu yi tsammanin yawan masu nema ko masu sha’awa ba a lokacin da muka fitar da EoI kamar mako guda bayan an naɗa ni,” inji shi yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today.
“Ya zuwa yau, muna da kimanin ‘yan Nijeriya miliyan 1.6 da suka nuna sha’awarsu, suka gaya mana abin da suke yi, suka gabatar da bayanan kuɗaɗen shigar su, da kuma abin da za su yi da bashin. Ba mu yi tsammanin wannan adadin ba.
“Don haka ina tsammanin mutane suna sauraron maganganun Shugaban Ƙasa kuma suna tsammanin hakan.”
Shugaban Ƙasa ya naɗa Nwagba a matsayin shugaban CREDICORP a ranar 5 ga Afrilu don jagorantar yunƙurin gwamnati mai ci na faɗaɗa samar da lamuni na mabuƙata ga ƴan Nijeriya masu aiki.
Kimanin watanni shida da naɗin nasa, ya ce ya shirya tsaf don aiwatar da aikin.