Back

‘Yan sanda na neman mutane 11 kan kashe-kashe a Plateau

A ranar Juma’a ne runduna ta musamman da ke wanzar da zaman lafiya a Filato da wasu sassan jihohin Bauchi da Kaduna, Operation Safe Haven (OPSH) ta bayyana cewa ana neman mutane 11 bisa zarginsu da hannu a hare-hare da kashe-kashe daban-daban, musamman a ƙananan hukumomin Barkin Ladi, Bassa, Bokkos da Riyom a Jihar Filato.

OPSH ta ce ana neman mutanen ne domin yi musu tambayoyi kan haɗin kansu a hare-haren da aka kai a wurare daban-daban a jihar.

Mataimakin Kwamandan Rundunar OPSH, Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda (DCP) Terzungwe Iyua, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar OPSH da ke Jos, ya ce tukuici mai kyau na jiran duk wanda ya taimaka wa hukuma wajen kama su.

Ya bayyana sunayen waɗanda ake nema a matsayin Muhammadu MP daga Bokkos mai lambar waya O9114827408; Muhammed wanda aka sani da MOPOL mai lambar waya 09126869112; Rabiu Ibrahim daga ƙauyukan Yelwa/Gashish/Nghar; Buba Sobe daga Tenti a Barkin Ladi, Senfos Inusa Gaine daga Zorgom da Nahaska Boderi shi ma daga Tenti, a Barkin Ladi.

Sauran sun haɗa da: Dudi Mohammadu daga unguwar Yamusa Bago a ƙauyen Machambe, Habu Mohammadu daga unguwar Yamusa Bago a ƙauyen Machambe, Ja’afaru Matakala daga unguwar Yamusa Bago a ƙauyen Machambe; Hassan Waje daga unguwar Yamusa Bago a ƙauyen Machambe da Sanusi Dafor daga ƙaramar hukumar Bokkos.

A cewar Mataimakin Kwamandan, duk da ƙoƙarin maido da zaman lafiya a yankin, waɗanda ake nema sun ci gaba da kawo cikas ga ci gaba.

Ya kuma ƙara da cewa, a bisa aikin rundunar ‘Operation SAFE HAVEN’, jami’an ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin an gurfanar da waɗanda suka aikata munanan laifuka domin fuskantar shari’a.

“Mun ci gaba da gudanar da ayyukan leƙen asiri, wanda ya kai ga kashe wasu daga cikin masu laifin da suka kai hare-haren.

“Kyakkyawan tukuici yana jiran kowane mutum ko gungun mutane, waɗanda suka ba da bayanai masu amfani da za su kai ga kama duk wanda ake tuhuma. Duk wanda yake da cikakken bayani kan inda waɗanda ake zargin suke, to ya tuntuɓi rundunar ‘Operation SAFE HAVEN’ da rundunar ‘yan sandan Nijeriya da sauran hukumomin tsaro,” inji DCP Iyua.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?