Back

‘Yan sanda sun bankaɗo ƙungiyar fataucin yara, sun kama Shehu Sani, da wasu mutane 3

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta bankaɗo wata ƙungiyar fataucin yara bayan ta kama wasu mutane huɗu da ake zargin ‘yan ƙungiyar ne ƙarƙashin jagorancin Malam Shehu Sani tare da kuɓutar da wata yarinya ‘yar shekara biyu mai suna Zainab.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna (PPRO), ASP Mansir Hassan, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya sanyawa hannu, kuma ya fitar a ranar Talata, inda ya ce ƙungiyar ta kan kai hari kan yara ƙanana, waɗanda su kaɗai ke kan titi, suna wasa ko kuma suna gudanar da sana’o’i.

“Suna yin garkuwa da waɗanda abin ya shafa suna ajiye su a wani wuri, yayin da suke neman mai sayan yaran kafin su sayar da su.

“Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ƙarƙashin haziƙin shugabancin Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, CP Ali Audu Dabigi, ta samu gagarumar nasara wajen yaƙi da safarar yara.

A ranar 24 ga Maris, 2024 da misalin awanni 1100, bisa rahotannin sirri, jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar cafke wata katafariyar ƙungiyar fataucin yara da ke aiki a jihar.

“Aikin ya yi sanadin ceto ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, mai suna Zainab Abdulhameed, ‘yar shekara 2. ’Yan ƙungiyar da aka kama a cikin aikin, sun amince da hannu a wannan mummunan aika-aikar.

Mutanen da aka kama sun haɗa da Shehu Sani mai shekaru 40 da ke zaune a Ungwan Rimi Kaduna; Tskan Isiaku mai shekaru 43, shima yana zaune a Ungwan Rimi Kaduna; Angela Onazu mai shekaru 44, zaune a Sabo Kaduna da Hafsat Hussaini mai shekaru 24, mazauna Ungwan Rimi Kaduna.

“Tsarin aikin ƙungiyar ya haɗa da kai hari ga yara ƙanana waɗanda ke su kaɗai a kan tituna ko aka aike su.

“Saboda haka, ya kamata iyaye da masu kula da su su kasance a ankare tare da lura da inda ’ya’yansu ko ‘yan riƙon su suke. Kamun na baya-bayan nan ya nuna gaskiyar hatsarori da yara ke fuskanta idan ba a kula da su ba, ko da na ɗan lokaci kaɗan. Ta hanyar faɗakarwa da kuma sa hannu sosai a cikin rayuwar ‘ya’yansu, iyaye da masu kulawa za su iya taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye su daga yuwuwar cutarwa.

“CP Ali Audu Dabigi ya yaba da ƙwazon jami’an ‘yan sandan da suka shiga aikin tare da jaddada ƙudirin rundunar na haɗa kai da al’umma domin tabbatar da tsaron dukkan mazauna yankin, musamman ma waɗanda suka fi kowa rauni a cikin al’umma. Tare, ta hanyar ƙara taka-tsantsan da haɗin gwiwa, za mu iya samar da yanayi mai aminci ga yaranmu domin su ci gaba,” inji ASP Hassan.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?