Back

‘Yan sanda sun bankaɗo wani shiri na haddasa ɓarna a lokacin Ƙaramar Sallah a Kano

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta ce ta gano wasu mutane da suke fakewa da wasu ƙungiyoyin addinin Islama domin tayar da tarzoma a lokacin bukukuwan Sallah.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammad Usaini Gumel ne ya bayyana haka a wata ganawa da ya yi da malaman addinin musulunci da kuma wakilai daga masarautun jihar biyar a ranar Litinin.

Sai dai ya bayar da tabbacin cewa ‘yan sanda sun yi gaggawar ɗaukar mataki kan masu aikata laifukan da ke ɓoyewa a tsakanin mutane masu bin doka da oda domin yin ɓarna a gabanin, lokacin da kuma bayan bukukuwan Sallah.

Ya bayyana Kano a matsayin jiha ɗaya tilo da babu ɗaya daga cikin ‘yan ƙasar da masu garkuwa da mutane ko ‘yan bindiga ke tsare da su, yana mai alaƙanta hakan da sa-idon jami’an tsaro.

Ya ce, “Muna da wasu sunaye da suke fakewa da ƙungiyar Ƙadiriyyar Musulunci suna ƙoƙarin kawo rashin jituwa. Don haka mun tattauna da shugaban ɗarikar, Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara, kuma ya nesanta kansa da su, har ma ya ba da izinin kamo duk wani mai ƙoƙarin kawo cikas ga zaman lafiya.”

Kwamishinan ‘yan sandan ya kuma yi nuni da cewa, sashen leƙen asiri na rundunar sun gano wasu ‘yan siyasar da ko dai ba su gamsu da yadda al’amura ke tafiya ba ko kuma ba su samu muƙamai ba da suka jajirce wajen haifar da rashin tabbas.

Ya ce, “Na umurci jami’an ‘yan sanda da su kama duk wanda suka samu da makami ko ƙoƙarin haifar da rashin tabbas a tsakanin mutane.”

Shi ma wanda ya wakilci Sarkin Bichi, Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (AIG), Bashir Albasu mai ritaya, ya yaba wa Kwamishinan ‘yan sandan kan tabbatar da zaman lafiya a Kano.

Ya amince da al’ummar Kano daban-daban da kwararowar ‘yan kasuwa akai-akai, da kuma yadda birnin ke fama da miyagun laifuka, amma ya tabbatar da aniyar masarautun biyar na tallafa wa ƙoƙarin tsaro domin ɗorewar zaman lafiya.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?