Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ekiti ta ce ta kama wasu mutane guda takwas da ake zargi da kisan wasu sarakunan gargajiya biyu da aka yi kwanan nan tare da sace wasu dalibai a jihar.
Ekiti dai ta sha fuskantar hare-hare kwanan nan. A ranar 29 ga watan Janairu, ‘yan bindiga sun kashe wasu sarakunan Ekiti guda biyu – Onimojo na Imojo, Oba Olatunde Olusola, da kuma Elesun na Esun Ekiti, Oba Babatunde Ogunsakin.
Hakazalika a yankin, maharan sun kai hari kan wata motar bas ɗin makaranta inda suka tafi da wasu ɗalibai biyar na Apostolic Faith Group of Schools, malamai uku, da direban bas ɗin.
Da take bayar da ƙarin haske a ranar Lahadin da ta gabata, Hukumar ‘Yan Sanda a Jihar Ekiti ta ce an kama waɗanda ake zargin ne a wani aikin haɗin gwiwa wanda aka gudanar ta dajin Emure-Ekiti, dajin Ise/Ogbese zuwa dajin Emure-Ile a jihar Ondo.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan, Abutu Sunday, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa harin ya haɗa da jami’an ‘yan sanda, jami’an Amotekun, ’yan banga, mafarauta na gida, mambobin Ƙungiyar Agbekoya da suka haɗa da ‘yan sanda da Amotekun Corps daga jihar Ondo.
Ya bayyana sunayen waɗanda ake zargin su ne Yaya Sumaila, Idrisu Abubakar, Hassan Abudullahi, Abudullahi Abudullahi, Haruna Abubakar, Usman Abudullahi, Haruna Sule, ciki har da wani Babusa Alhaji Lede da aka kama a cikin dajin Ayedun/ Ayebode Ekiti a yankin Ikole na jihar.
“A halin yanzu ana ci gaba da binciken waɗanda ake zargin kuma suna bayar da sahihan bayanai da za su iya kai ga kama wasu da suka gudu waɗanda ake zargin aikata ta’asar,” in ji shi.
“Yayin da rundunar ba za ta huta ba har sai an sa ’yan fashin da suka gudu su fuskanci fushin doka, ana kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da tallafa wa ‘yan sanda da sahihan bayanai masu inganci da kuma suke kan lokaci da za su kai ga kama waɗanda ke bayan waɗannan munanan ayyuka da sauran miyagun laifuka a jihar”.
Abubuwan da aka samu daga hannun waɗanda ake zargin sun haɗa da saniya ɗaya, adda guda uku, gatari ɗaya, wuƙa ɗaya da kuma kayan abinci.