Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke wani mutum mai suna Habu Ibrahim dan shekaru arba’in bisa zargin shi da sawa matar shi guba a abinci a kauyen Danadama da ke karamar hukumar Sule Tankarkar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, A T. Abdullahi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce an kama wanda ake zargin ne bisa zargin shi da hada abin sha da nama da guba, inda ya nufi matar shi mai suna Zakiya Uzairu ‘yar shekaru talatin da biyar da nufin ya ci gadon dukiyarta.
Ya ce da samun rahoton, sai jami’an tsaro na sashen Sule Tankarkar suka yi gaggawar kama wanda ake zargin a wurin.
CP. Abdullahi ya ce an kawo wanda ake zargin ofishin ‘yan sanda shiyya da ke Sule Tankarkar domin yi masa tambayoyi, daga bisani kuma aka mika shi zuwa sashin binciken manyan laifuka na jiha (SCID) da ke Dutse don ci gaba da bincike.
“Lokacin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amince da aikata laifin, inda ya tabbatar da sahihancin bayanan da aka baiwa ‘yan sanda.
“Ya amince da niyyar kashe matar shidomin ya mallaki dabbobin ta, da suka hada da awaki, tumaki, da shanu.
“Ya ce matar da kyar ta tsere bayan ta gane gubar kuma ta fahimci manufar shi,” in ji ‘yan sandan.