Back

‘Yan sanda sun ceto daya daga cikin mutane uku da aka sace a masallaci a Zamfara

Wasu gungun jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara sun yi nasarar kubutar da mutum daya daga cikin mutane uku da aka sace a masallaci a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara. Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, ASP. Yazid Abubakar ne ya bayyana haka a yau ranar Juma’a.

Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da sace wasu dattijai uku a masallacin da ke garin Tsafe sabanin yadda ake yada labaran da ke nuni da cewa mutanen da aka sace na da yawa.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 29 ga watan Fabrairu, 2024 da misalin karfe 5:00 na safe a lokacin da masallata ke taruwa a masallacin Juma’a domin yin sallar asuba, amma abin ya rutsa da su sakamakon bayyanar wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, wadanda ake zargin ‘yan bindiga ne dauke da manyan makamai.

Wadanda ake zargin sun kutsa cikin masallacin ne da ke kan hanyar asibitin da ke karamar hukumar tsafe da nufin ci gaba da yin garkuwa da su, amma masu ibadar sun yi nasarar tserewa sai dai wasu dattijai uku wadanda aka Yi awon gaba da su aka kai su inda ba a sani ba.

Duk da haka, bayan samun bayanai, jami’an ‘yan sandan cikin gaggawa sai suka mayar da martani da  dabarun irin na tsaro suka shiga aikin bincike da ceto.

Tawagar ‘yan sandan ta bi bayan Wadanda ake zargin ‘yan bindigar ne dajin Dangajeru inda suka martanin su ya tilastawa ‘yan bindigar barin daya daga cikin mutane ukun da suka Gaza sari irin na ‘yan bindigar, inda Kuma aka ceto shi.

A cewar ‘yan sanda mutumin da aka ceto ya sake ya koma ga iyalan shi bayan an duba lafiyar shi.

Ana ci gaba da aikin ceto sauran mutanen da aka sace.

A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Shehu Dalijan ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa, rundunar tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar za su yi duk abin da ya dace domin ganin an dawo da zaman lafiya a jihar

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?