Back

‘Yan sanda sun damke mutum goma da laifin satar yara ar’ba’in da biyar, sun kwato shida a Jihar Nasarawa

CP Shehu Nadada, kwamishinan jihar Nasarawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta damke wasu mutane guda goma da ake zargi da satar yara da ba su gaza ar’ba’in da biyar ba da kuma sayar da su.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Shehu Nadada, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar rundunar da ke Lafiya, da yammancin ranar Jumma’a.

A cewar kwamishinan, jami’an ‘yan sanda da ke aiki da shiyya ta Keffi da ke sintiri na yau da kullum a ranar goma ga watan Janairu, sun kubutar da wani mutum daga hannun fusatattunjsma’a, bayan anyi bincike sai rundunar ta gano cewa ya sato wani yaro ne dan shekara biyar daga Keffi.

Ya ce daga baya wanda ake zargin ya amsa cewa yana daya daga cikin wata kungiyar da ta kware wajen satar yara da sayarwa ga wanda ya yi tayi mafi yawa.

Nadada ya ce binciken da aka yi ya kai ga kama wasu ‘yan kungiyar mutane tara.

Ya ce, da aka yi bincike cikin wayar salular wadanda ake zargin an gano cewa sun yi awon gaba da yara ar’ba’in da biyar da suka dauko ba bisa ka’ida ba a fadin kasar nan.

Kwamishinan wanda bai bayyana tsawon lokacin da aka sace yaran ba, ya ce yawancin su an sace su ne daga jihohin Abuja, Kaduna, Nasarawa, Filato da Neja.

Ya bayyana cewa an kwato shida daga cikin yaran daga Abuja, Ondo da kuma jihar Legas, yayin da ake ci gaba da bincike domin a Kara kamo wasu da ke da hannu cikin satar yaran.

Ya ci gaba da cewa wadanda ake zargin sun amsa laifin sayar da yara da dama a kan farashi daban-daban, daga Naira dubu dari uku da hamsin zuwa Naira miliyan miliyan daya da rabi. Farashin ya danganta da shekarun da kuma jinsin su.

Nadada ya ce, wadanda ake zargin yawanci suna hada baki ne da wasu jami’an jin dadin al’umma wajen samar da takardun bogi wadanda za su saukaka siyar da yaran ga masu saye.

Kwamishinan ya kuma bukaci iyaye da su kara maida hankali a unguwannin su tare da yin kira ga masu neman daukar yara da su yi hattara da masu aikata laifuka

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?