Back

‘Yan sanda sun kai farmaki maɓoyar masu garkuwa da mutane a Legas, sun kama mutum 3

Rundunar ‘yan sandan Jihar Legas ta tabbatar da cafke wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a yankin Ijanikin da ke jihar.

Jami’ar Hulɗa da Jama’a na Shiyyar (ZPRO), SP Umma Ayuba, ta tabbatar da kamun a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba a Legas.

Ta bayyana sunayen waɗanda ake zargin Samuel Kwasi, mai shekaru 64; Monday Unachukwu, mai shekaru 24; da Freeman Ekpebo, mai shekaru 23.

ZPPRO ɗin ta ce Jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Shiyya ta 2, Onikan, Legas, sun kai farmaki maɓoyar masu garkuwa da mutanen da ke unguwar Ijanikin, inda suka kame ƙungiyar, tare da ceto wasu mutane biyu a wani samamen gaggawa.

Ta ce waɗanda ake zargin sun yi garkuwa da mutane biyu tare da neman naira miliyan 150.

“A ranar 26 ga Maris, da ƙarfe 6 na yamma, wata ‘yar unguwar Millionaire Estate, Oniru, Legas, ta kai rahoton sace ɗanta mai shekara 10, ‘yar aiki (an ɓoye sunansu saboda dalilai na tsaro), da direba, Mista Samuel Kwasi, a unguwar Ikoyi a Legas.

“Ta kuma bayyana cewa masu garkuwa da mutane sun buƙaci a biya su naira miliyan 150.

“Tare da aiki da wannan bayanan sirrin, wata tawagar jami’an tsaro ƙarƙashin jagorancin CSP Tijjani Taofiq (Jami’in da ke Kula da Sashin Sa ido na Shiyya), sun yi gaggawar yin amfani da dabarun bin diddigi da tattara bayanan sirri,” inji ta.

Ayuba ta ce rundunar ta gano maɓoyar masu garkuwa da mutanen ne a unguwar Ayetoro da ke Ijanikin, Badagry Road, Legas.

“A ranar 28 ga Maris, da ƙarfe 3:40 na rana, jami’ansu sun kai farmaki maɓoyar da ke Otal ɗin Cozzy, Ijanikin, inda aka kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin, Unachukwu, inda aka ceto waɗanda aka sace ba tare da wani lahani ba.

“A wani aiki na haɗin gwiwa, an kama direban, Kwasi da Ekpebo a Otal ɗin Sun Era, Ijanikin, inda ake zargin suna jiran karɓar kuɗin fansa,” inji ta.

A cewar ZPRO, bincike ya nuna cewa Kwasi shine babban wanda ake zargi kuma shi ne ya shirya garkuwar.

“Kwasi ya amsa laifin lalata na’urar bin diddigin motar kafin aikin.

“An gano na’urar bin diddigin motar da wuƙa a daƙin otal da ke Sun Era Hotel, Ijanikin, inda waɗanda ake zargin suka kama,” inji ta.

Ayuba ya ce Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (AIG) mai kula da shiyyar, Mista Olatoye Durosinmi, ya yaba wa jami’an ‘yan sandan bisa gaggauwa da suka yi, sannan ya kuma yabawa al’ummar bisa haɗin kai da kuma taka-tsantsan.

Ta ce AIG ɗin ya kuma buƙaci iyaye da masu kulawa da su yi taka-tsan-tsan tare da gudanar da cikakken bincike a lokacin ɗaukar ma’aikatan gida.

A cewarta, rundunar ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaro ga ɗaukacin mazauna jihohin Legas da Ogun.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?