Back

‘Yan sanda sun kama ɗalibai 2 bisa zargin sace kansu

Rundunar ‘Yan Sanda a jihar Legas ta ce ta kama wasu ɗalibai biyu bisa zargin ƙaryar cewa an sace su.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya, NAN, ranar Alhamis, a Legas.

Hundeyin ya ci gaba da shaida wa NAN cewa waɗanda ake zargin sun kuma buƙaci iyayensu da su biya dala 100,000 (kimanin naira miliyan 150).

Ya bayyana sunayen waɗanda ake zargin da Ayodele Balogun, ɗan shekara 21, ɗalibi mai mataki 200 a fannin Ilimi a Jami’ar Jihar Legas, Ijaniki, da abokinsa, Dennis Okuomo, mai shekaru 21, ɗalibin NIIT Legas.

A cewarsa, dukkansu sun yi ƙaryar cewa an sace su, inda suka buƙaci naira miliyan 150 domin su taimaka wa abokin nasu, Ayodele, wanda ɗan gidan talakawa ne.

“Dennis ne ya bayar da shawarar saboda Ayodele ɗan gidan talakawa ne kuma babban abokinsa; ya so ya yi amfani da ƙaryar don tara masa kuɗi domin ya sami damar kula da iyalinsa.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce a ranar 2 ga watan Fabrairu, Ayodele ya ɓace daga gida, yayin da Dennis ya yi amfani da wayar Ayodele ya sanar da mahaifinsa, Mista Balogun, game da satar bogi na ɗansa, kuma ya nemi kuɗin fansa dala 20,000 (kimanin naira miliyan 30).

Hundeyin ya ce waɗanda ake zargin sun umurci mahaifin Ayodele da ya biya kuɗin fansa ta hanyar Bitcoin, asusun da suka aika masa a lokacin da Ayodele ke ɓoye a ɗakin Dennis a otal ɗin mahaifin Dennis.

“Mahaifin Ayodele, Direban wani kamfani mai zaman kansa, ya samu labarin tare da damuwa da yawa, yana mamakin inda zai tara dala 20,000.”

Hundeyin ya ce a lokacin da Balogun ya kasa tara kuɗin, Dennis ya yanke shawarar ya yi ƙaryar cewa an sace shi, inda ya buƙaci mahaifinsa ya ba shi dala 100,000 (kimanin naira miliyan 150).

A cewarsa, dukkan waɗanda ake zargin sun yanke shawarar barin otal ɗin ne domin ɓuya a cikin wani daji inda suka zauna har na tsawon kwanaki biyar yayin da ake ci gaba da tattaunawa da bincike.

“A ranar 16 ga Maris, da yake ba a biya kuɗi ba kuma waɗanda ake zargin ba su gamsu da yanayin daji ba, sai suka yanke shawarar komawa ɗakin Dennis a otal ɗin mahaifinsa.

“Sun shaida wa kowa cewa sun tsere ne daga wurin masu garkuwa da mutane, kuma da sauri suka kira mahaifin Ayodele su sanar da shi cewa sun tsere daga wurin masu garkuwa da mutane.”

Sun kai Ayodele asibiti da imanin cewa ya fito ne daga wurin masu garkuwa da mutane.

“Bincike ya zuwa yanzu ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun yi ƙaryar cewa an sace su ne.

“Suna hannunmu, mutane biyu da suka sace kansu,” inji shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?