Back

‘Yan sanda sun kama mutane 85 a maɓoyar masu aikata laifuka a Abuja

Aƙalla mutane 85 ne aka kama a lokacin da jami’an ‘yan sanda suka kai samame maɓoyar masu aikata laifuka a Durumi da Dei-Dei a Abuja, babban birnin ƙasar.

‘Yan sanda sun ce wuraren da aka kama waɗanda ake zargin da aikata laifuka daban-daban sun zama wuraren hutu na ‘yan tada zaune tsayen. Daga cikin laifuffukan, ana zargin su da kafa haramtattun gine-gine da gidajen kwana, safarar miyagun ƙwayoyi da ƙera kuɗaɗen jabu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan FCT, SP Josephine Adeh, ta ce an gudanar da aikin ne tsakanin ranar 31 ga Maris zuwa 4 ga Afrilu, 2024.

Ta ce, “An aiwatar da bincike a wasu gine-ginen da kuma ƙwato shaidu da dama da suka haɗa da kuɗaɗen takarda da na ƙwandala na jabu na gida da na waje, makamai, babura takwas, janareta bakwai, na’urori, da katunan ATM da dama da ake zargin an sace su ne daga waɗanda abin ya shafa.”

Adeh ta ƙara da cewa duk waɗanda aka kama za a tantance su, yayin da waɗanda aka samu da laifin za a bayyana su a gurfanar da su a gaban kotu.

Ta ci gaba da cewa, an tarwatsa tare da ƙona haramtattun gine-ginen katako da masu aikata laifukan suka gina don hana masu laifi daga mayar da waɗannan wuraren zuwa wani wuraren aikata laifuka.

A halin da ake ciki, Kwamishinan ‘Yan Sanda na Babban Birnin Tarayya, CP Ben Igweh ya tabbatar wa mazauna yankin ƙudurin sa na fatattakar masu aikata laifuka a Babban Birnin Tarayya da kuma tabbatar da tsaron kowa da kowa.

Ya kuma buƙaci mazauna yankin da su lura da kuma amfani da layukan gaggawa na ’yan sanda don bayar da rahoton abubuwan zargi ta hanyar 08032003913, 08028940883, 08061581938, 07057337653 PCB: 090222222352, CRU: 31810, CRU: 08028940883.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?