Back

‘Yan sanda sun kama mutane biyar, sun kwato kayan abinci na majalisar dinkin duniya da za a kaiwa ‘yan gudun hijira

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da karkatar da buhunan alkama na hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya UNWFP, tare da gano buhunan alkama kusan dubu daya da dari biyu da talatin da takwas a Fatakwal.

Kakakin rundunar na ƙasa, ACP Olumuyiwa Adejobi ya ce kimanin buhunan alkama dubu daya da dari takwas da ar’ba’in ne wadanda za a yi jigilar su daga tashar Ibeto, Fatakwal, zuwa sansanin ‘yan gudun hijira (IDP) da ke jihar Kano direbobin da aka dorawa wannan aikin suka karkatar da su ta hanyar damfara gami da haɗin bakin abokan aikin su.

Ya ce jami’an ‘yan sandan Najeriya da ke da alaka da tashar jiragen ruwa ta Gabas ne suka cafke wadanda ake zargin tare da kama su a ranar shida ga watan nan.

Wadanda ake zargin sun hada da Umar Hashim, Edidiong Umoh, Udah Stanley, Abubakar Jariri da Yunusa Babangida.

Sauran abubuwan aka damke tare da buhunan alkama guda dubu daya da dari biyu da talatin da takwas da aka sace, sun hada da babbar mota da wata motar safa da aka yi amfani da su wajen aikata laifin.

Rundunar ta ‘yan sandan ta ce an mayar da buhunan alkama da aka kwato ga hukumar samar da abinci ta duniya, kuma ana kokarin kwato buhunan alkama guda dari shida da biyu da suka bata tare da kama sauran wadanda ake zargi da aikata laifin.

A halin da ake ciki, babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya sake jaddada manufar ‘yan sandan Najeriya na ganin an hukunta masu hannu a cikin ayyukan zagon kasa ga tattalin arzikin kasa da kuma sanya wahalhalun rayuwa a cikin jama’a masu rauni.

Don haka, Egbetokun, ya bayar da umarnin gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike tare da daure duk masu hannun a cikin lamarin dai-dai da hukuncin da doka ta ƙasa ta tanada.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?