‘Yan sanda a Abuja sun kama wasu mutane 15 da ake zargi da wawashe wata ma’ajiyar kayayyaki a garin.
A safiyar Lahadi ne waɗansu mazauna garin suka wawashe ma’ajiyar kayayyaki na Sashin Kula da Noma na FCT a unguwar Tasha a Abuja.
Sai dai sa’o’i kaɗan bayan faruwar lamarin, rundunar ‘yan sandan FCT ta ce an kama mutane 15 da suka wawashe ma’ajiyar.
A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce, “Rundunar ‘yan sandan FCT ta samu cikakken bayani game da harin bazata da wasu fusatattun mutane suka kai a ma’ajiyar kayan abinci na Sashin Kula da Noma na FCT da ke Tasha, Abuja, a ranar 2 ga Maris, 2024, wanda ya yi sanadin ɓarna da wawashe ma’ajiyar.
“Rundunar tana so ta bayyana cewa tun daga lokacin an dawo da zaman lafiya a yankin kuma an shawo kan lamarin sosai, domin an kama mutum goma sha biyar da ake zargi, ciki har da jami’an tsaro biyu da masu kula da ma’ajiyar suka ɗauka aiki.
“An ƙwato kayayyakin shaida irin su buhunan masara guda ashirin da shida, babura biyar, da wasu lalatattun kwanon rufi daga hannun waɗanda ake zargin.”
Wawashe ma’ajiyar da aka yi a ranar Lahadi ya faru ne a daidai lokacin da ake fama da matsalar matsin tattalin arziki a Najeriya.
Alƙaluman hauhawar farashin kayayyaki ya kai wani sabon mataki, inda ya kai kashi 29.90 cikin 100 a Janairu da tsadar rayuwa ta yi tashin gwauron zabi tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya bayyana kawo ƙarshen biyan tallafin man fetur.
Matakin da gwamnatinsa ta ɗauka a kan Naira ya ƙara dagula lamarin, inda ya haifar da zanga-zanga a sassa da dama na ƙasar.
Gwamnatin Tarayya ta shigo cikin gaggawa don rage tasirin sauye-sauyen, da ɓullo da abubuwan rage raɗaɗin matsalar da sauran matakan, amma da alama sun yi kaɗan don magance matsalar.
A makon da ya gabata ne Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta yi zanga-zanga a faɗin ƙasar kan gazawar gwamnati wajen biyan buƙatun ƙungiyar sakamakon cire tallafin man fetur da kuma wahalhalun da ake fuskanta.
Sai dai Shugaba Tinubu yana kira ne da a yi haƙuri don sauye-sauyen gwamnatinsa su samu gindin zama, yana mai jaddada cewa babu gudu babu ja da baya kan matakan da ya ɗauka.