Back

‘Yan sanda sun kama wanda ya shirya harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna a 2022 da satar ɗaliban Jami’ar Greenfield

Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ta ce jami’anta sun kama wani Ibrahim Abdullahi, wanda aka fi sani da Mande, wanda ake kyautata zaton shi ne ya shirya harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna a watan Maris ɗin 2022 da kuma sacewa da kashe ɗaliban Jami’ar Greenfield da kuma sace-sacen da aka yi kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

An kama Mande tare da wasu da dama da ake zargi.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a Jihar Kaduna.

Da yake gabatar da waɗanda ake zargin a Hedikwatar ‘Yan Sandan Kaduna a ranar Alhamis, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, Muyiwa Adejobi, ya ce an kama Mande ne bisa wasu sahihan bayanai a gadar sama ta hanyar Abuja zuwa Kaduna a Rido Junction a ƙaramar hukumar Chikun.

Ya ƙara da cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa na kasancewa shugaban ƙungiyar masu garkuwa da mutane da ke addabar hanyar Kaduna zuwa Abuja kuma ya shiga cikin manyan ‘yan bindiga kamar Dogo Gide da Bello Turji.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?