Jami’an tsaro na hedikwatar shiyya ta Owerri reshen Jihar Imo ta hanyar sahihan bayanan sirri da bincike mai zurfi sun kama wani fitaccen ɗan fashi da makami mai suna Izea John Chukwuebuka ‘m’ mai shekaru 23 a unguwar Asa a ƙaramar hukumar Ohaji Egbema.
A cewar mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, ASP Henry Okoye, wanda ake zargin wanda aka kama a wani samame na haɗin gwiwa tare da ‘yan banga na yankin a ranar Talata 9 ga watan Afrilu, 2024, ya amsa laifin yin fashi da makami a kasuwar Alaba, kasuwar Douglas, Tetlow, da sauran wuraren kasuwanci a jihar.
“Ya yarda cewa yana da wata ƙungiya a Kasuwar Hausa ta Ama, wacce ke karɓar kayan sata a wajensa domin samun kuɗi.
“Ana ci gaba da ƙoƙarin kamo ‘yan ƙungiyarsa gaba ɗaya, musamman masu karɓar kayan sata, masu sayarwa, da masu ƙera bindigogin gida. Za a miƙa wanda ake zargin ga hedikwatar jihar domin ƙarfafa binciken da ake yi, kuma za a gurfanar da shi gaban kuliya bayan kammala cikakken bincike,” inji shi.
Kayayyakin da aka ƙwato daga wurin da aka aikata laifin sun haɗa da bindiga guda ɗaya na gida da harsashai guda biyu.
A halin da ake ciki, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Imo, CP Aboki Danjuma, ya tabbatar wa ‘yan kasuwa da sauran mazauna jihar ta Imo cewa, rundunar ‘yan sandan za ta ci gaba da ruɓanya ƙoƙarinta na samar da yanayi mai aminci da tsaro don ci gaban harkokin zamantakewa da tattalin arziƙi a jihar.
Ya kuma tabbatar da cewa rundunar ta jajirce wajen ganin ta daƙile ƙungiyoyin masu aikata laifuka da ba su tuba ba a jihar.