Back

‘Yan sanda sun kama wani mutum da ya kashe matarsa ​​a Adamawa

Rundunar ‘yan sandan Jihar Adamawa ta cafke wani magidanci mai suna Riba Kwanta mai shekaru 40 ɗan asalin garin Bode a ƙaramar hukumar Shelleng a jihar bisa laifin kashe matarsa ​​mai suna Godiya Akwale.

Ana zargin Kwanta da datse kan matar sa da adda sannan ya kulle gawarta a cikin gidan su kafin ya gudu zuwa Jihar Ondo.

Ma’auratan sun yi aure sama da shekara uku.

Kakakin rundunar ‘yan sandan SP Suleiman Yahaya Nguroje ya tabbatar da kama wanda ake zargin.

Ya bada tabbacin za a gurfanar da Kwanta gaban kotu bayan kammala bincike.

Ya ce, “Ya zargi matar tasa da yin dare da wata ƙawarta, dalilin da ya sa ya daddatsa wuyanta har ya kai ga halaka ta, ya kulle ta a ɗakin kwanan su, ya tsere zuwa Jihar Ondo.

“Ya aikata laifin ne a ranar 3 ga watan Disamba, 2023 a gidansu na Bode dake ƙaramar hukumar Shelleng.”

Nguroje ya ƙara da cewa Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, Dankombo Morris ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin tare da gurfanar da wanda ake zargin.

“Hakazalika CP ya buƙaci jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu,” inji Nguroje.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?