Back

‘Yan sanda sun kama wani tsohon kanar na soja da matar shi kan zargin buga  kudaden bogi

Rundunar ‘yan sanda ta Zone 2, Onikan, Legas, ta cafke wani tsohon kanar na soja da matar shi bisa mallakar na’urar buga takardun kudaden bogi.

Kamar yadda kamfanin dillancin labaru na Najeriya ya ruwaito, ‘yan sandan sun gabatar da wadanda ake zargi a kan laifuka dabam-dabam, ciki har da ma’auratan mai shekaru hamsin da matar mai shekaru ar’ba’in da shida a hedikwatar rundunar da ke Legas  a ranar Juma’a.

Jami’in hulda da jama’a na shiyyar, Tunni Ayuba, wanda ya yi magana a madadin mataimakin sufeto-janar na ‘yan sanda mai kula da shiyyar, Olatoye Durosinmi, ya ce kama na’urar buga takardun ne ya kai ga cafke tsohon sojan da matar ta shi.

Ayuba ya ce rundunar ta dauki matakin ne a ranar uku ga watan Fabrairu, inda ta kai farmaki maboyar na’urar buga takardun a tsibirin Legas, inda ta kama Mai bugawar sanadiyyar wani rahoton sirri da mataimakin sufeto Janar na ‘yan Sanda AIG ya amince da shi.

Kakakin ya ce, rundunar ‘yan sandan ta kuma kwace wata na’ura da ake zargin na’urar ce ake yin amfani da ita wajen buga zaren tsaro a kan jabun kudaden, sannan ta kwato kudi saifa CFA miliyan dari uku da kuma Naira miliyan tara, wadanda ake zargin jabu ne da aka buga da na’urar.

A cewar Ayuba, mai na’urar buga takardun ya amsa cewa ya shafe sama da shekaru uku yana buga jabun kudaden, ya kuma bayyana sunayen dillalan shi da yake baiwa kudaden na bogi su rarraba.

Rundunar ta kara da cewa ” bayanan shi da ya yi ne ya kai ga kama ma’auratan, wadanda abokan aikin su ne na aikata laifuka.”

Ta kuma bayyana cewa ikirari da ma’auratan suka yi ne ya sa aka kama tsohon sojan da aka gano yana da wasu da ake zargin jabun kudade ne na gida da na waje ne a lokacin da aka binciki gidan shi.

A cewar ta, ana ci gaba da kokarin kamo ‘yan kungiyar da suka gudu.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?