
*…Kamar yadda CP ya bukaci al’umma da su kula da mutanen da suke ba wa wayoyin hannun su domin yin kira.
‘Yan sanda sun kama wasu mutane uku da ake zargi da yin garkuwa tare da kashe Dan makwabcin su, Abdullahi Sani dan shekara sha hudu. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP. Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ranar Alhamis.
Binciken farko a cewar KIyawa ya kai ga cafke babban wanda ake zargin, Ismail Adamu, mai shekaru 22, daga unguwar Hotoron Fulani a garin Kano.
Tun da farko dai rundunar ‘yan sandan ta samu korafi daga mahaifin wanda aka kashen, Alhaji Rabi’u Abdullahi, shi ma mazaunin Hotoron Fulani a cikin birnin Kano inda ya bayyana wa ‘yan sandan cewa wani da ba a san ko wane ne ba ya bugo masa waya yana neman a biya shi Naira miliyan hudu domin ya sako masa dan shi, Abdullahi Sani na wanda suka yi garkuwa da shi.

Kwamishinan ‘yan sanda, Mohammed Usaini Gumel, ya yi gaggawar tada tawagar ‘yan sanda daga sashin yaki na dakile masu garkuwa da mutane na rundunar domin tabbatar da ceto wanda aka sace tare da damke wadanda suka aikata wannan aika-aika inda aka yi nasarar cafke wanda ake zargin.
Babban wanda ake zargin, Ismail Adamu ya amsa cewa ya hada baki da wani Mai suna Risi, dan unguwar Mariri Quarters Kano tare da yin garkuwa da wanda aka kashe.
Wanda ake zargin ya ci gaba da cewa sun kai wanda aka kashen zuwa kauyen Sabuwar Zara inda suka daba masa wuka a wuyan shi suka jefa shi a cikin wani ramin ban daji, cikin wani gini da ba a kammala shi ba, daga bisani kuma suka tuntubi mahaifin shi suka bukaci ya biya kudin fansa Naira Miliyan hudu a sake shi.
Rundunar ‘yan sandan ta ziyarci wurin da lamarin ya faru inda aka fito da gawar marigayin daga ramin aka kai shi asibitin kwararru na Abdullahi Wase Kano inda wani likita ya tabbatar da mutuwar shi. An ajiye shi a dakin ajiyar gawa na Asibiti.
Binciken da aka yi cikin hankali ya kai ga kama wasu abokan haɗin bakin Wanda ake zargin guda biyu, Musa Usman mai shekaru goma sha bakwai a Hotoron Fulanin, da Abdullahi Usman mai shekaru ashirin wanda ya taimaka wa babban wanda ake zargin ya yi sulhu ya wayar salular.
Za a gurfanar da wandanda ake zargin zuwa kotu bayan an kammala bincike.
Police Nab 3 Suspects For Kidnapping, Killing Their Neighbors 14 Year Old Son
*…As CP urged citizens to be mindful of the people they give their mobile phones to make calls*
Three suspects were arrested by the Police for kidnapping and Killing of their neighbors fourteen year old son Abdullahi Sani. Kano state command’s Police Public Relations officer, SP. Abdullahi Haruna KIyawa has disclosed Thursday.
Preliminary investigations according to KIyawa led to the arrest of the principal suspect; Ismail Adamu, aged 22, of Hotoron Fulani Quarters, Kano.
Earlier, the police has received complaint from the father of the victim, Alhaji Rabiu Abdullahi, a resident of Hotoron Fulani Quarters in Kano metropolis disclosing to the police that he had received a phone call from an unknown person demanding four million Naira ransom for his son, Abdullahi Sani of same address whom they kidnapped.
The Commissioner of Police, Mohammed Usaini Gumel, immidiately mobilized a team of Policemen from the Anti-Kidnapping Unit of the Command to ensure the rescue of the victim and arrest the perpetrators which led to the arrest of the suspect.
The principal suspect, Ismail Adamu confessed to have conspired with, Risi, male of Mariri Quarters Kano and kidnapped the victim.
The suspect further revealed that they took the victim to Sabuwar Zara Village where they stabbed him on his neck and threw him inside a Soakaway in an uncompleted building and later contacted his father and demanded the ransom for his release.
The Police visited the crime scene where the deceased body was exhumed from a Soakaway and evacuated same to Abdullahi Wase Specialists Hospital Kano where a Medical doctor certified him dead. He was deposited at the Hospital’s Mortuary.
Discreet investigation led to the arrest of two other collaborators, Musa Usman, aged 17, of Hotoron Fulani Quarters Kano, and Abdullahi Usman, aged 20 of the same address who assisted the principal suspect to negotiated the ransom with their mobile phone.
The suspect will be charged to court upon completion of the investigation.