Back

‘Yan sanda sun kama wasu sojoji biyu na bogi a Legas

Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta kama wasu sojoji biyu na bogi da ake zargin sun yi barazanar kashe wani mutum da wuƙa a lokacin da suke faɗa.

Mai Magana da Yawun Rundunar ’Yan sandan Jihar, SP Benjamin Hundeyin, wanda ya tabbatar da hakan a Legas yau Laraba, ya ce waɗanda ake zargin suna hannun ‘yan sanda tun ranar Litinin.

Hundeyin ya ce, rundunar ‘yan sanda ta Isolo a ranar Litinin da ta gabata da misalin ƙarfe goma da rabi na dare, ta samu labarin cewa ana faɗa a titin Aina, unguwar Isolo a Legas.

Ya ce nan take aka tura tawagar ‘yan sintiri zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya.

Mai Magana da Yawun ya ce a lokacin da ‘yan sandan suka isa wurin, sun gano cewa an ga wani Ben Okafor, wanda ya yi iƙirarin cewa shi Kofur ne a rundunar sojojin Nijeriya, da wuƙa, tare da wani Darlinton Ihenacho.

Hundeyin ya ce an ga mutanen biyu suna faɗa da wani Oludotun, wanda daga baya ya kai ƙara ga ‘yan sanda cewa wani soja ya bi shi da wuƙa, yana barazanar kashe shi.

“Bayan an kama waɗanda ake zargin tare da bincike su, an samu katin shaidar sojan Najeriya na bogi, mai ɗauke da Cpl. Geoffrey Emmanuel, mai lamba 140861, wuƙa, da ruwan barkono a hannunsu.

“Za a gurfanar da waɗanda ake tuhuma a kotu idan aka kammala bincike.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?