Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wasu ‘yan baranda da dama da ake zargin an dauko du haya ne domin kawo cikas ga sake gudanar da zabukan da ke gudana a wasu sassan jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mohammed Usaini Gumel wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai, ya ce ‘yan barandan da aka kama da makamai, ana zargin wani dan siyasa ne da ya tsaya takara a zaben ya dauke su aikin hargitsi.
An kama su ne a kusa da unguwar Kunchi/Tsanyawa, daya daga cikin mazabar jihar Kano da ake sake zaben.
Gumel ya ce, “mun ga wata babbar mota da ta lalace a gefen hanya. Mun ga mutane da yawa a gefen hanya. Da farko mun yi tunanin cewa man motar ne ya kare. Amma da muka lura da kyau, sai muka gano suna boye da makamai.”
Kwamishinan yace, “Wani Abdulrazaq Muhammad wanda aka fi sani da Mai Salati, daga cikin garin Kano ya shaida mana cewa wani Gwarmai da ke takara a yankin ne ya gayyace su.”
“Za mu sa Gwarmai ya san ko shi dan takara ne na gaske ko kuma yayi mana bayanin kan me ya sa ya gayyace su yankin.”
“Muna zargin suna cikin daji ne domin yi wa jami’an zabe kwanton bauna a kan hanyarsu ta zuwa gabatar da sakamakon zaben,” in ji kwamishina ‘yan sandan, Gumel.