Back

‘Yan sanda sun kama wasu ‘yan sanda da ake zargin su da ƙwacen Naira miliyan talatin a Abuja

An kama wasu Jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya (NPF) na musamman a Abuja da laifin ƙwacen naira miliyan talatin daga hannun wani ɗan ƙasa.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

A cewar Adejobi, an kawo wa rundunar ƙarar ƙwacen ne ta dandalin X, kuma NPF ta kama jami’an da abokan aikin su waɗanda tun farko suka tsere bayan an fara bincike.

Sanarwar ta ce, “Bayan wani ƙwace da wasu jami’an ‘yan sandan Najeriya da ke aiki da rundunar ‘yan sanda ta musamman a Abuja suka yi a baya-bayan nan da suka yi wa wani mutum ƙwacen kuɗi Naira miliyan talatin da dubu ɗari uku, wanda aka sanar wa rundunar ta dandalin X, rundunar ‘yan sandan Najeriya na son bayyanawa da kuma sanar da cewa an samu gagarumin ci gaba wajen damƙe jami’an da ke da alhakin aikata wannan ta’asa ta rashin da’a, kasancewar an kama rundunar da aka fara gudanar da bincike a farko, kuma a halin yanzu tana tsare.

“Sfeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, a wani ɓangare na ƙudirinsa na tabbatar da bin doka da oda a cikin rundunar ‘yan sandan Najeriya, ya bayar da umarnin fara shari’ar ladabtarwa domin tabbatar da an yi adalci cikin gaggawa.

“Waɗannan matakan ladabtar da su na nuna rashin amincewa na rundunar ‘yan sandan Najeriya da duk wani nau’i na rashin ɗa’a ko almundahana a tsakanin jami’anta.

“Shugaban rundunar ya kuma jaddada wajabcin cewa waɗanda aka samu da laifin karya amanar da jama’a suka ba su na fuskantar cikakken sakamakon abin da suka aikata, domin irin wannan ɗabi’a bata kawai ɓata sunan rundunar, har ma tana lalata ƙokarin haɗin gwiwa na tabbatar da doka da oda a ƙasar mu.

“NPF ta fahimci cewa gaskiya da riƙon amana ne kan gaba wajen riƙe amanar jama’a kuma za ta ci gaba da ɗaukar ƙwararan matakai kan duk wani rashin ɗa’a da ke tsakanin mu.”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?