Back

‘Yan sanda sun kama wata mata da ta ‘sace’ kanta, da wasu mutane 52

‘Yan sanda a Akwa Ibom sun ceto mutane huɗu da aka sace. Ɗaya daga cikinsu ita ce macen da ta yi ƙaryar an sace ta.

Sun kuma kama mutane 52 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Mista Waheed Ayilara, ya shaidawa manema labarai a Uyo ranar Juma’a cewa wasu laifukan sun haɗa da kisan kai, garkuwa da mutane, fashi da makami, safarar yara, ƙungiyar asiri da kuma zamba.

Ya ce ɗaya daga cikin waɗanda sace, wata mata ce daga ƙauyen Nung Oku a ƙaramar hukumar Ibesikpo Asutan ta Akwa Ibom wacce ta shirya satar nata.

Daga nan sai ta buƙaci a biya ta naira miliyan 4, amma ‘yan sanda sun kama ta.

“An samu rahoton a ranar Litinin daga wani Enobong Sampson cewa an sace ‘yar uwarta kuma masu garkuwa da mutanen suna neman naira miliyan 4 a matsayin kuɗin fansa.

“Sakamakon haka, Jami’an Hukumar Yaƙi da Garkuwa da Mutane ta Rundunar ‘Yan Sanda suka fara wani gagarumin aiki da bayanan sirri domin zaƙulo masu garkuwa da mutanen tare da kuɓutar da wanda aka sace.

“A ranar Talata, an kama wacce ake zargin da saurayinta a wata maɓoya da ke Mbierebe Obio a ƙaramar hukumar Ibesikpo Asutan.

“Ta amsa laifin haɗa baki da saurayinta da wasu mutane uku domin su ce sun sace ta don samun kuɗi a wajen gwaggon ta dake wajen ƙasar,” inji Ayilara.

Ya ƙara da cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne ‘yan sanda suka kama wani mutum a ƙauyen Uruting da ke ƙaramar hukumar Okobo a jihar bisa laifin kashe mahaifinsa mai shekaru 75 da haihuwa, ta hanyar amfani da adda.

Wanda ake zargin ya yi iƙirarin cewa dalilin da ya sa ya ɗauki matakin da ya ɗauka shine saboda mahaifinsa da ya rasu ya sayar da dukkanin filayen da yake da su, ciki har da wanda ya ba shi domin ya gina gidansa, inji kwamishinan ‘yan sandan.

Ayilara ya kuma ce, a ranar 8 ga watan Maris, ‘yan sanda sun kama wani mutum ɗaya a ƙauyen Ayam da ke ƙaramar hukumar Etinan a jihar da laifin samar da lalatattun kayan marmari da kayayyakin jabu.

Har ila yau, a ranar 8 ga Maris, ‘yan sanda sun ceto tare da kama wani mutum da ya yi amfani da na’urar POS wajen damfarar ‘yan ƙasa da ba su ji ba, wanda za a ƙone shi amma zuwan jami’an ‘yan sanda ya daƙile faruwar hakan.

Ayilara ya ce yawancin waɗanda abin ya shafa sun tantance shi kuma an ƙwato kuɗi naira 350,000 daga hannun sa a lokacin da aka kama shi.

Kwamishinan ‘yan sandan ya yi alƙwarin cewa za a gurfanar da duk waɗanda ake zargin da zarar an kammala bincike.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?