Rundunar ‘yan sanda a jihar Enugu ta ce ta kai samame maɓoyar Ƙungiyar Masu Fafutukar Kafa Ƙasar Biafra (IPOB) da maɓoyar Ƙungiyar Tsaro ta Gabas (ESN) a yankin Akwuke a cikin birnin Enugu.
Jami’an ‘yan sandan dai sun gamu da tirjiya daga ‘yan tawayen, inda suka buɗe wuta a lokacin da suka gansu, amma ƙarfin wuta na ‘yan sandan ya ci ƙarfinsu, lamarin da ya kai ga halaka biyu daga cikin ‘yan ƙungiyar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Daniel Ndukwe, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, inda ya ce ‘yan sandan sun kai samame ne a ranar Asabar da misalin ƙarfe 2:30 na safe.
Ndukwe ya ce sauran ’yan haramtacciyar ƙungiyar sun tsere da raunukan harbin bindiga daban-daban.
Ya ce an ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, Sub-Machine Gun (SMG) guda ɗaya, Pump-Action Gun (PAG) guda ɗaya, alburusai masu girman 7.62 mm bayan samamen da sojojin suka yi.
A cewarsa, ’yan sanda sun kuma gano wasu harsashe masu rai guda biyar da wani ƙaramin Littafi Mai Tsarki na Kiristoci mai launin shuɗi wanda mai yiwuwa ana amfani da shi wajen ɓoye abubuwan da ake zargin layya ne.
“A bisa tsarin rigakafin da kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Kanayo Uzuegbu ya ɓullo da shi, jami’an ‘yan sandan da ke yaƙi da ƙungiyoyi masu tsatstsauran ra’ayi sun kai wani samame a wata maɓoyar ƙungiyar IPOB/ESN a unguwar Akwuke a cikin birnin Enugu.
“Bincike na farko ya nuna cewa an goge lambar AK-47 da aka ƙwato.
“Masu aikata miyagun laifuka ne ke da alhakin kai hare-hare da dama tare da yin awon gaba da bindigu na jami’an ‘yan sanda. Ana ci gaba da gudanar da bincike.” inji shi.