
Nigerian Police Vehicle
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ta sanar da bayar da tukwicin Naira miliyan hamsin ga duk wanda ya bayar da bayanai masu muhimmanci da za su kai ga kama wasu ‘yan fashi biyu a Katsina.
Mutanen da ake nema ruwa a jallo a cewar wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar, sun haɗa da Modi Modi da Jan Kare, waɗanda ke aiki a cikin jihar Katsina, musamman a yankunan ƙananan hukumomin Kankara da Safana.
“Kiyaye zaman lafiyar mazauna jihar na da matuƙar muhimmanci kuma Gwamnatin Jihar Katsina da Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina da sauran jami’an tsaro a jihar sun duƙufa wajen ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki kan masu aikata miyagun laifuka da ke yin barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin mazauna jihar.
“Wannan tukwicin shaida ne kan sadaukarwar da muka yi na tabbatar da adalci, kasancewar lamarin tsaro aiki ne na haɗin gwiwa.
“Wannan shiri na da nufin inganta ayyukan tsaro a jiharmu da yaƙi da ayyukan waɗannan miyagun mutanen.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Za a kiyaye asalin mai ba da labarin da bayanan da aka bayar cikin sirri don tabbatar da tsaronsu da kariyarsu.”
Ya ƙara da cewa, an ƙarfafa wa dukkan ‘yan ƙasar da abin ya shafa da su fito da duk wani bayani da ya dace da zai taimaka wa jami’an tsaro wajen kamo masu shirya waɗannan munanan laifuka na garkuwa da mutane da kuma fashi.
“Don duk wani bincike ko bada bayanai, a tuntuɓi hedikwatar rundunar ko kuma hedikwatar hukumar tsaro mafi kusa ko a kira lambobin kamar haka 07015142112 08023871144,” in ji sanarwar.
A baya-bayan nan dai jihar Katsina ta sha fama da hare-haren ‘yan bindiga a sassa daban-daban, inda gwamnan jihar, Malam Dikko Umaru Radda ya nemi goyon bayan gwamnatin tarayya domin shawo kan matsalar.