Back

‘Yan sanda sun sako shugaban jam’iyyar Labour Party Yau

Shugaban jam’iyyar Labour Party na kasa, Julius Abure, wanda jami’an hedikwatar ‘yan sanda na shiyya ta 5 suka kama a ranar Laraba a Benin, babban birnin jihar Edo, ya samu ‘yanci ta hanyar beli.

An samu labarin cewa ‘yan sandan sun kama shi ne sakamakon wata takardar koke da aka aikewa shiyyar daga ofishin babban sufeto janar na ‘yan sanda a Abuja.

Bayan an sake shi da misalin karfe biyu na daren Alhamis, Abure, yayi jawabi ga magoya bayan shi, ya ce fafutukar kwatar ‘yancin  ‘yan kasa ba ya samuwa cikin sauki.

Ya ce takura shi da ake yi da nufin tayar da zaune tsaye, a rikirkita jam’iyyar shi, an fara ne tun bayan babban zaben shekarar da ta gabata.

Abure ya ce har yanzu shugaban jam’iyyar na jihar Edo, Kelly Ogbaloi, da shugaban matasan jihar na tsare kuma da alama za a sake su a yau.

Ya ce, “Bari in jinjina muku saboda hadin kai da goyon baya da jajircewar ku. Babu gwagwarmayar kwato kasa da ke zuwa cikin sauki. A kasashen duniya da dama da masu fafutukar ‘yanci suka yi gwagwarmayar kwato ‘yan kasar su, masu fafutukar neman ‘yanci sun yi fama da rashin adalci, suna fuskantar shari’a da kuma abin da ke faruwa da ni da sauran abokan aikina tun bayan zaben shekarar da ta wuce.”

“Bayan zaben duk gari sun yi ta kokarin tada rikici a jam’iyyar mu. Su yi ƙoƙari su kawo mana zargin ƙarya. Sun kawo zargin amfani da jabun takardu a kan mu ba tare da zargin yayi tasiri ba. Sun zo da maganar almubazzaranci.”

“Duk mutumin da ya fusata a cikin jam’iyyar, sai su je su tunzura shi, su rubuta mana koke. Abin ban mamaki shi ne, ‘yan sanda ma sun yi aiki da waɗannan, sun gano cewa waɗannan abubuwan ƙarya ne.”

“A jiya muna shirye-shiryen gudanar da zaben fidda gwani na jihar Edo, kuma ba shakka ‘yan sanda sun kama mu, sun kama mu bisa abin da ba zan so tattaunawa a yanzu ba saboda har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike don haka ba za mu so mu yi riga-kafi ba.”

“Amma dole ne in bayyana a fili cewa, bayan shiga tsakani da dama da aka yi, dun bayar da beli na, sai dai shugaban jam’iyyar na jihar Edo, Kelly Ogbaloi da shugaban matasa. Su (‘yan sanda) sun kuma yi alkawarin cewa zuwa safiyar ranar Alhamis za su sake su. Muna fatan za su cika alkawari su sake su.”

“Duk abin da ke faruwa da ni ba zai sa ni karaya daga gwagwarmayar ba. Dole ne mu ci gaba da bin manufar jama’a. Dole ne mu ci gaba da gwagwatmaya domin ceton al’ummar mu har sai mun kwato masu ‘yanci. Na fada, kuma zan sake faɗa, ba kwace mulki ne ke da muhimmanci ba. Muhimmin abu shine yadda za ku tafi da mulkin.

“A yau APC ce ke kan mulki. Rayuwa ta ƙara zama wahala ga mutane. A yau ana musayar dala kusan N2,000. Ana sayar da man fetur a yau kan Naira dari bakwai kowace lita. Akwai ma karancin man a halin yanzu, kuma da alama farashin zai sake karuwa.”

“Haba farashin kayayyaki, duk ya ninka sai biyu, amma yanzu ya haura kashi talatin da daya cikin dari, rashin aikin yi ya karu, kuma buhun shinkafa a yau ana sayar da shi kan Naira dubu dari da ashirin bayan mafi karancin albashi Naira dubu talatin ne. ka ga abin da ke faruwa. Ka ga abin ban haushi kuma ‘yan Nijeriya sun shiga tsaka mai wuya.”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?