Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kano ta shirya tsaf domin samar da isasshen tsaro kafin zuwa ziyara da kuma lokacin ziyarar Sanata Godwin Akpabio jihar a gobe ranar Asabar biyu ga wannan watan domin halartar taro karo na talatin da takwas na Jami’ar Bayero ta Kano.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Usaini Gumel ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da manema Labarai a ranar Juma’a.
Gumel ya ce, an samar da ingantattun tsarin ayyuka kan yadda za a samar da tsaron a kowane wurin da ake sa ran shugaban kasa Sen.
Ya kuma tabbatar da cewa rundunar ta samar da matakan tsaro na musamman domin tabbatar da ziyarar ta kasance cikin kwanciyar hankali da kuma lumana.
“Mun tattara isassun jami’ai masu dauke da makamai domin samar da tsaro ga shugaban Sanatocin kasar mu kafin ziyarar, da lokacin ziyarar da kuma bayan ziyarar,” in ji Gumel.
Gumel ya bayyana cewa tuni aka bayar da umarnin gudanar da aiki ga dukkan kwamandojin yankuna da aka nada, da kwamandojin dabaru, da jami’an ‘yan sanda na sassan kananan hukumomin Fagge, Gwale da Kumbosto a cikin birnin.
Ya Kara da cewa, a halin yanzu rundunar tana aiki tare da sauran hukumomin tsaro a jihar don tabbatar da zirga-zirgar jama’a ba tare da rikici ba ga duk mutanen da suka halarci taron.
“Mun tattara isassun jami’an tsaro da za su samar da tsaro a dukkan tituna da mahadar da ke kan hanyar zuwa cibiyar daga filin jirgin sama na Malam Aminu da sauran tashoshin kasa.”
Kwamishinan ya kuma ce tuni rundunar ta fara gudanar da sintiri mai tsauri tare da sauran jami’an tsaro domin nuna shirin jami’an na ziyarar.
Ya bayyana cewa an dauki matakan ne da nufin baiwa mazauna jihar damar tarbar shugaban Sanatocin ba tare da wata barazana ta tsaro ba.
Kwamishinan ya shawarci shugabannin jam’iyyun siyasar jihar da su ja hankalin magoya bayan su da su guji duk wani nau’in tashin hankali na ‘yan daba kafin ziyarar, da kuma bayan ziyarar Sanatan.
Gumel ya ce: “Ba za mu amince da duk wani aiki da zai kawo rudani kafin ziyarar, lokacin da kuma bayan ziyarar ba.”
Ya yi gargadin cewa duk wani mutum ko kungiyoyin da aka samu suna kokarin tayar da zane tsaye za a kama su kuma a gurfanar da su a gaban kuliya.
Kwamishinan ya ce a lokacin ziyarar shugaban majalisar dattawan, shi da kan shi zai je jami’ar Bayero domin halartar taron karo na talatin da takwas da jami’ar za ta yi da kuma bayar da shaidar digiri na uku ga mataimakin shi Sanata Barau Jibril da dai sauran su.