Back

‘Yan Sanda sun tabbatar da ‘yan Bindiga sun kashe jami’an su biyu a Zamfara, basu Tantance satar mutum ar’ba’in ba

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da kisan jami’an ta guda biyu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka yi kisan a ranar Talata lokacin da ‘Yan taddar suka kai hari kauyen Kasuwar Daji da ke karamar hukumar Kauran Namoda a Jihar Zamfara.

Kakakin rundunar, SP. Yazid Abubakar wanda ya bada tabbacin hakan ga Btvhausa ta wayar tarho yace, I zuwa yanzu ba a tantance adadin mutanen da ‘yan bindigar suka yi awon gaba da su ba.

Rahotonin da aka samu daga wasu mazauna yankin bayan harin na ranar Talata sun ce ‘yan bindigar da suka afkawa kauyen Kasuwar Dajin sun yi awon gaba da mutane sama da arba’in da suka hada da mutane ashirin ‘yan gida daya.

Sharahu Almajir Kasuwar daji, babban amini ne kuma ‘Dan uwa ne ga wasu da abin ya shafa ya bayyana hakan ta kafar sada zumunta ta Facebook inda ya ce, “’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane sama da 40 daga ‘yan uwana, dana (SALIM) ciki har da mahaifiyar matata marigayiya, tare da ‘ya’yan ta mata da dama a garin, ‘yan gidajen makwab ta. An kashe wasu ‘yan sanda biyu da dan uwan mu, Umar Habi.”

Wata majiya mai tushe da ba a bayyana sunan ta ba, a hira da muka yi ta wayar tarho, ta ce wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai farmaki kauyen a ranar Talata domin daukar fansa.

Sai dai a cewar majiyar ba gaskiya ba ne cewa akwai tsohon shugaban ƙungiyar motocin sufuri, (NURTW) Alhaji Hamisu Kasuwar Daji wanda majiyar ta tabbatar da cewa yana ƙasar Makka a lokacin da abin ya faru duk da cewa an sace mutane mafi yawa ‘yan gidan shi da suka hada da ‘ya’yan shi da matan shi guda biyu da wadanda suka dogara da shi.

A cewar majiyar, “an yi garkuwa da mutane 21 daga cikin iyalan tsohon shugaban kungiyar ma’aikatan sufuri ta kasa (NURTW), Alhaji Hamisu Kasuwar Daji, wadanda suka hada da matan shi biyu, ‘ya’yansa 13, dan uwa da kuma wadanda suka dogara da shi.”

“ kwatsam, ‘yan bindigar suka iso kauyen, suka kai farmaki ofishin ‘yan sanda da ke gidan Alhaji Hamisu Kasuwar Daji. Suka shiga gidan suka sace mata biyu. Matar ta uku ta yi sa’a, ‘yan fashin sun kasa samun damar shiga dakinta.” Inji majiyar 

Ya ce, “Sun kuma binciki gidaje da dama a kusa da su inda suka yi awon gaba da mutane da yawa kafin su bar kauyen. Harin ya firgita mu.” 

SP. Yazid Abubakar ya bayyana mana cewa rundunar ‘yan Sandan Jihar na ci gaba da bincike da bin diddigin ‘yan ta’addan domin kwato wadanda aka sacen, Kuma a Kamo masu aikata laifin domin gurfana da su a gaban kuliya.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?