Rundunar ‘yan sandan Nijeriya, reshen Jihar Kano, ta sha alwashin yin biyayya ga umarnin Kotun Tarayya da ta hana Gwamnatin Jihar Kano aiwatar da dokar da ta rushe Masarautun Kano.
A ranar Alhamis ne wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta bayar da wata sabuwar doka da ta hana Gwamna Abba Yusuf mayar da Sarki Muhammadu Sanusi II kan kujerarsa.
Mai Shari’a Mohammed Liman wanda ya bayar da umurnin ya kuma dakatar da aiwatar da sabuwar dokar da ta rushe masarautun Bichi, Gaya, Karaye, da Rano.
Sai dai a yayin da ya ke miƙa wa Sanusi wasiƙar sake naɗa shi ranar Juma’a, Gwamna Abba Yusuf ya yi watsi da wannan umarni, inda ya ce alƙalin ya bayar da ita ne daga Amurka.
Daga baya sarki Sanusi ya jagoranci sallar Juma’a a gidan gwamnati kafin ya wuce fadar.
Sai dai da yake jawabi ga manema labarai a hedikwatar rundunar a safiyar ranar Asabar, Kwamishinan ‘Yan Sandan, Usaini Mohammed Gumel, ya gargaɗi masu tayar da ƙayar baya.
Ya ce, “Rundunar ‘yan sanda na yin biyayya ga umarnin kotu mai lamba FHC/KN/CS/182/2024 mai kwanan wata 23 ga Mayu, 2024 da Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta bayar tare da jami’an tsaro a jihar.
“Saboda haka, muna kira ga jama’a da su sani cewa ‘yan sanda a jihar suna aiki tare da sojoji da sauran jami’an tsaro kuma suna da cikakken ƙarfin samar da ingantaccen tsaro ga kowa da kowa kamar yadda muka himmatu wajen aiwatar da ayyukan mu kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya ya tanada.”
“Saboda haka, kamar yadda rundunar ‘yan sanda ke jagorantar sauran jami’an tsaro domin wanzar da zaman lafiya domin cimma matsaya, ya kamata ’yan ɓata-gari su nisanta kansu daga tashe-tashen hankula a duk inda suke, kuma kada su yi amfani da halin da ake ciki su kai farmaki kan jama’a, dukiya da kayayyakin more rayuwa na Jiha.
“Duk mutumin da aka samu da irin wannan hali za a yi maganinsa kamar yadda dokar ƙasa ta tanada,” inji shi.