Back

‘Yan sandan Babban Birnin Tarayya sun kama masu safarar yara 2, sun miƙa su da yaran ga ‘yan sandan Sokoto

Jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja sun kama wasu mutane biyu da ake zargin masu safarar yara ne: Kulu Dongonyaro da Elizabeth Ojah, a yayin da suke ɗauke da yara biyar zuwa yankin.

Jami’ar Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan (PPRO), SP Josephine Adeh, a wata sanarwa da ta rabawa manema labarai a Abuja, ta ce: “Jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja, a ranar 27 ga Afrilu, 2024, da misalin ƙarfe 8:00 na dare, sun cafke wasu mata biyu da ake zargi, Kulu Dogonyaro da Elizabeth Ojah, dangane da safarar yara biyar.

“Waɗanda ake zargin da suka yi yunƙurin tsere wa kamun jami’an ‘yan sandan Sakkwato, jami’an ’yan sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ne suka kama su a mahaɗar Kagini, Abuja, a yayin da suke ɗauke da yara biyar (5) zuwa Babban Birnin Tarayyan.

“Rundunar ‘yan sandan, ta miƙa waɗanda ake zargi da waɗanda abin ya shafa ga rundunar ‘yan sandan Jihar Sakkwato domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da su gaban kotu.

“Kwamishanan ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, CP Benneth C. Igweh, ya buƙaci iyaye da su mai da hankali sosai ga ‘ya’yan su tare da jaddada ƙudirin sa na tabbatar da tsaron mazauna Babban Birnin Tarayya.

“Ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su yi taka-tsan-tsan tare da yin amfani da layukan gaggawa na ‘yan sanda wajen bayar da rahoton abubuwan da ake zargi ta hanyar: 08032003913, 08028940883, 08061581938, da 07057337653 PCB: 09022222352, 1902222352.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?