Back

‘Yan ta’adda sun kai hari mahaifar Ƙaramin Ministan Tsaro, sun sace sama da mutane 50

Da sanyin safiyar Juma’a ne wasu gungun ‘yan ta’adda suka mamaye garin Maradun, hedikwatar ƙaramar hukumar Maradun a Jihar Zamfara inda suka yi garkuwa da mutane sama da 50, galibi mata.

Maradun ita ce mahaifar Ƙaramin Ministan Tsaro na Nijeriya, Honorable Bello Muhammad Matawalle.

Wani mazaunin yankin mai suna Malam Sulaiman Maradun a wata tattaunawa ta wayar tarho ya shaidawa wakilin Blueprint cewa ‘yan ta’addan sun yiwa garin kawanya da misalin ƙarfe 12 na safe inda suka fara gudanar da ayyukan gida-gida.

“Abin takaici ne yadda suka afka garinmu saboda sun zo da wasu makamai kuma suka fara harbe-harbe a iska da tsakar daren yau Juma’a,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa ‘yan ta’addan sun kashe mutane 10 tare da yin awon gaba da dabbobin jama’ar yankin da har yanzu ba a tantance adadin su ba.

Ya ce ‘yan ta’addan sun kai hari fadar Sarkin Maradun, Alhaji Garba Tambari, a lokacin da sarkin baya nan.

“A yanzu haka mutane da yawa galibi mata ne waɗannan ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a yayin harin kuma yawancin mutanen mu sun ɓace kuma ba inda za a same su kawo yanzu,” inji shi.

“Wannan ba shi ne karon farko da waɗannan ‘yan ta’adda da ake fargabar ke kai hari a yankin Maradun ba. Ya kamata gwamnati a dukkan matakai su ɗauki tsauraran matakai don magance matsalar rashin tsaro da ke addabar yankinmu.”

Maradun ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da na Jihar Zamfara da su ƙara tura dakaru zuwa yankin domin kare jama’a daga munanan ayyukan ‘yan ta’adda da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.

Ƙoƙarin jin ta bakin Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, Asp Yazid Abubakar, ya ci tura, saboda ba a samu dukkan layukan sa ba yayin da ake haɗa rahoton.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?