Masu garkuwa da mutane sun sako tara daga cikin ɗalibai 21 da aka yi garkuwa da su a Jami’ar Tarayya Gusau a jihar Zamfara.
Ɗaya daga cikin masu sasantawa da ya nemi a sakaya sunansa ya ce sakin ɗaliban tara ya biyo bayan tattaunawa mai tsanani na tsawon watanni huɗu.
Ɗaliban sun shafe kwanaki 178 a sansanin ‘yan ta’addan bayan sace su da aka yi a watan Satumban 2023.
An sace ɗaliban ne a lokacin da ‘yan ta’adda suka kai hari a wani ɗakin kwanan ɗalibai da ke Sabon Gida, wata al’umma da ke kusa da jami’ar a babban birnin jihar Zamfara a watan Satumban shekarar da ta gabata, suka yi awon gaba da ɗalibai da wasu mutanen garin.
Bayan ‘yan sa’o’i kaɗan, jami’an tsaro sun ceto wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa.
Mai sasantawar ya shaida cewa ‘yan ta’addan sun bayyana ƙarara bayan sace su cewa manufar su ba kuɗi ba ce.
“Mun fara tattaunawa da su kai tsaye bayan an ɗauki ɗaliban. Tun farko sun ƙi haƙura amma da muka matsa sai suka saurare mu,” inji shi.
Ya ce Ali Kawaje, shugaban ƙungiyar ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa, ya fusata da Gwamnatin Tarayya da na jihar Zamfara saboda kama ɗan uwansa da aka yi.
“Ya dage cewa dole ne mu gyara,” inji mai sasantawar, yana neman a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro.
Mai sasantawar ya ce bayan kashe Kawaje a wani samame da Sojojin Saman Nijeriya suka kai musu, an fara tattaunawa ne bayan da sabon kwamandan ƙungiyar ya dage cewa ba za a sako ɗaliban ba.
“Mun ɗauki makonni kafin mu shawo kansa, tare da taimakon wasu shugabannin Fulani. Da muka ci gaba da tattaunawa, sai suka dage cewa ba wai don kuɗi ne aka sace su ba, sai dai don jami’an tsaro su sako wasu ‘yan uwansu.
“An sako waɗannan ɗalibai tara ne a wani ɓangare na alƙawurran da wasu shugabannin Fulani da muka shiga sasantawar suka yi,” inji shi.
Da aka tambaye shi ko akwai kuɗi a lamarin, mai sasantawar ya ce ‘yan ta’addan da kansu “sun bayyana a fili tun da farko” cewa basu buƙatar kuɗi a lamarin.
“Hatta mutanen da suke cewa ya kamata Gwamnatin Tarayya ta saki, har yanzu ba mu san ko su waye suke magana ba. Don haka, ba mu yi magana da gwamnati game da kuɗi ba kuma na biyu, babu musayar fursunoni. Abin da zan iya gaya muku ke nan,” inji shi.
‘Yan ta’addan sun riƙe ɗaliban ne a dajin Babbar Doka da ke kusa da jihar Kaduna. An sake su da yammacin ranar Juma’a kuma aka miƙa su ga masu sasantawar.
“Wannan wani ɓangare ne na alƙawarin kuma mun yi imanin cewa da yardar Allah za su sake wasu. Muna fatan cewa tare da sa hannun Mai Ba Da Shawara kan Harkokin Tsaro na Ƙasa , za mu yi ƙari. Abu mafi muhimmanci shi ne babu kuɗi a cikin aikin,” inji shi.
An tattaro cewa an miƙa ɗaliban ga hukumomin tsaro waɗanda ake sa ran za su miƙa su ga gwamnatin jihar a yau.
Da aka tuntuɓi Kakakin Jami’ar, Usman Umar, ya ce ba a yi masa bayani ba game da sakin ɗaliban.
“Na kuma ga bayanai game da sakin ɗaliban kamar yadda kuka ce amma masu gudanarwar jami’an basu yi min bayani ba.”
Ƙungiyar da ta yi garkuwan ta na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin ta’addanci da ke aiki a arewacin Nijeriya.
Ƙungiyoyin ta’addancin sun kwashe sama da shekaru goma suna tada zaune tsaye a kan mazauna garin wanda ya yi sanadiyar mutuwa ko kuma raba dubban ɗaruruwan mutane da muhallansu.
Ƙungiyoyin ‘yan ta’addan da ake kira ‘yan bindiga a cikin gida, sun bambanta da ƙungiyar ta’addancin Boko Haram da ke kai hare-hare a yankin arewa maso gabashin Nijeriya, kuma ta yi sanadin mutuwar dubban mutane.
Tun a shekarar 2020 ne ake ci gaba da samun yawaitar garkuwa da ɗalibai a yankin arewa maso yammacin Nijeriya da kuma arewa ta tsakiyar Nijeriya, baya ga sace ɗalibai sama da 300 a Katsina, ‘yan ta’adda sun yi garkuwa da ɗalibai sau biyu a Nijar, sau uku a Kaduna, sau huɗu a Zamfara, sau ɗaya a Sokoto.
An yi garkuwa da ɗalibai na baya-bayan nan a garin Kuriga da ke jihar Kaduna a arewa maso yammacin Nijeriya. Sama da ɗalibai 200 har yanzu ba a sake su ba.